Friday, 24 September, 2021

Ads Banner

Mata da Miji Sun Saci Jariri Domin su Raineshi yazama Dansu A jihar Kano


Rundunar yansandan jihar kano sun damke wata mata da mijinta bayan da aka kamasu sun saci jaririn wani mutumi da matarsa ta haifa masa yan biyu.

Kakakin hukumar yansandan jihar kano,Dsp abdullahi haruna kiyawa ya bayyana sunan mijin da abubakar sadiq itakuma matar da maryam sadiq.

A cewarsa, matar ta bayyana cewa mijinnata ne yasa ta sato jaririn domin bashi da da namiji kuma yadade yananema.

Yakara da cewa Abubakar da matarsa sun shirya walima da wuri sun gayyato mutane suna cewa sun samu karuwa.

Hakanne yasa mutane suke sukafara zarginsu domin ansan maryam batada juna biyu.

A ranar ne kuma, dsp abdullahi kiyawa yace aka kaimasa rahoton satar jariri guda daya.

Uban yaron da aka sace ne mai uuna rabi’u Muhammad yakaiwa rundunar yansandan kara domin a bincika masa inda dansa yake.

Yace mai kula da jariran (surukarsa)ce tabuge da bacci, tana farkawa kuma taga babu jinjiri daya.

Yanzu haka dai an mayar da yaron wurin iyayensa,sukuma matar da mijin suna gaban hukuma.

0 comments on “Mata da Miji Sun Saci Jariri Domin su Raineshi yazama Dansu A jihar Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *