KannywoodLabaran Duniya

Dalilin da yasa amare basa cin kazar da ango ke kawowa a daren farko

Dalilin da yasa amare basa cin kazar da ango ke kawowa a daren farko

Kasancewar siyen baki abu mai matukar muhimmanci ga dukkan sabon aure musamman ma ranar da aka raka ango a daren farko.

Har wa yau yana daga cikin tsarin siyen baki a wurin ango idan zai shigo ya taho da gasasshiyar kaza. Wannan kaza ana kallon ta ne a matsayin Mabudin sabuwar rayuwa tsakanin amarya da ango a kasar Hausa.

Sai dai kuma duk da wannan kazar da ake siyowa amarya a daren farko, mafi yawan amare basa iya sakin jiki su ci wannan kazar yadda ya kamata. Shi ko minene dalilin da yasa amare ke nokewa su ki cin wannan kazar a daren farko?

Wani labarin a cikin bidiyo:

A wani labarin na ban mamaki kuma>>Wani kare ya mutu har lahira bayan ya shinshini dan kampai

Dalilai biyu da ke sanya amarya bata cin kazar da ango ke kawowa a daren farko.

Mutane da dama sun yi tsokaci dangane da yadda batun cin kaza ya ke zama kalubale ga amare a daren farko, daga cikin wadannan dalilai kuwa akwai wasu kamar haka:

  • Wasu na ganin babban dalilin da yasa amare basa iya cin kazar da ango ke kawowa a daren farko shi ne kunya. Sanin kowane cewa malam bahaushe na da matuƙar alkunya. sakamakon haka ne ma ya sanya idan an kawowa amare kaza a daren farko basa iya sakin jiki su ci. Saboda haka suna jin kunya ne sosai shi ne dalilin da yasa kamar yadda mafi yawan mata basa iya cin kaza.
  • Abu na biyu kuma shi ne, wasu na ganin cewa akwai tunanin cewa idan amarya ta yarda ta ci wannan kazar, to tamkar ta bayar da kanta ne saboda haka ango zai samu damar haike mata ya wajajjageta kamar yadda ta wajajjagi kazar. Wannan khudubar ana yawan yiwa amare ita a kasar Hausa wanda kuma hakan na sanya musu tsoro a cikin zukatansu sai su fassara daren farkon a matsayin wani dare da za su sha wahala sosai a hannun angunansu, wanda hakan na sanya samun sabani a gidan aure tun a daren farko.

Labari daga: Legit Hausa

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button