Kalaman SoyayyaLabaran Duniya

Ango ya bukaci a masa ragi ko musaya saboda amaryar ta masa tsada

Ango ya bukaci a masa ragi ko musaya saboda amaryar ta masa tsada

Wani lamari mai jan hankali da ya faru tsakanin wasu masoya 2 ya ja hankalin Al’umma sosai. Kamar dai yadda rahoton ya bayyana, wani Ango ya bukaci a masa ragi ko musaya saboda amaryar ta masa tsada.

Tun farko dai angon shi ne ya fara ganin amaryar tasa tun lokacin tana budurwa ya kuma nuna yana sonta har ya sanar da ita. Sai dai kuma kafin amaryar tasa ta amince masa sai da ta ja masa aji sosai, sai kuma daga baya ne ta amince masa domin ganin yadda ya nace mata.

Bayan wannan amaryar ta amincewa angonta sun fara Soyayya tun su na a saurayi da budurwa sai kuma ya zamanto tana yawan ja masa aji tare da yi masa abubuwa na wulakanci da kuma raunin hankali kala daban daban. To amma sakamakon so da kaunar da ya ke mata shi yasa ya rufe ido bai kula da hakan ba.

Ita kuma sai ta yi amfani da wannan damar wajen cin mutuncin sa tare da musguna masa. Kamar yadda wani rahoto ya bayyana, an taba samun wata rana da ya suma saboda ta ce ta fasa aurensa.

Bayan ya je zance a kofar gidan su amaryar tasa sai wata magana ta shiga tsakanin su wadda bata yiwa amaryar dadi ba a lokacin, sakamakon haka sai ta fusata ta ce ta fasa aurensa.

A dalilin haka ne angon ya shiga rudani wanda daga baya har ya kaishi ga faduwa kasa a sume bayan ta tara dukkan danganta ta kuma shaida musu matsayar ta kan batun auren nata da shi. Bayan ya fadi kasa a some sai da dangin amaryar tasa su ka kaishi asibiti domin ceto rayuwarsa.

Karanta>> Anyiwa uwar gida tsirara bayan an ba hamata iska da dangin amarya

Ango ya ce amarya ta masa tsada a ranar aurensu

Bayan duk wulakanci da wannan angon ya jurewa a wurin wannan baiwar Allah sai ranar da aka daura auren nasu bayan abokai sun taki shi sun fita, sai kuma ya zauna a kuryar kujera  3 sitter sai kuma ya kurawa amaryar tasa ido sosai na tsawon lokaci ko kiftawa baya yi.

Hakan ya sanya amaryar ta yi karfin hali ta tambayeshi lafiya kuwa ya ke kura mata ido tamkar wanda zai hadiyeta?

Budurwar idon angon sai yace wai daman duk wahalar da ya sha kan Soyayyar ta wannan shi ne karshen abun?

Nan take sai ya ce wallahi ba zai taba lamunta da wannan tsarin ba saboda shi ta yi masa tsada sai dai a yi masa rago ko kuma a yi masa musanya da wata daga cikin wasu yan matan da ke gidan su amaryar amma ba ita ba.

Wannan batu ba karamin tayar da hankali da kuma mamaki ya baiwa dukkan dangin amaryar ba.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button