Labaran Duniya

SUBHANALLAHI : An Cafke Wata Mata Mai Kaiwa Yan ta’adda Yayanta ana Lalata Dasu.

Jami’an hukumar yan sanda sun cafke wata mata mai suna mariya, Bisa zarginta da Daukar yayanta da kuma na yan’uwanta zuwa cikin daji gurin yan bindiga suna lalata dasu.

A wani Rahoto Da mujallar Arewa Media Ta fitar a Shafinta Na Facebook ya bayyana cewa, Matar Tanayiwa Yan bindiga Safarar yan matan zuwa dajin Galadimawa inda acan ake aikata alfashar dasu.

Bayan Da Rundunar Yan sanda ta IRT wacce babban sifetan yan sanda yakafa ta binciki mai laifin, matar ta amsa laifinta inda ta bayyana yanda son zuciya ya rufe mata idanu har ta aikata wannan aika-aika.

Matar Ta bayyana yanda takeyi tana kaiwa yan bindigar yayan nata da kuma na yan’uwanta kafin dubunta yacika yan sanda suyi ram da ita.

Matar da ake zargi mai suna mariya

 

SUBHANALLAHI : An Cafke Wata Mata Mai Kaiwa Yan ta’adda Yayanta ana Lalata Dasu.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button