Kannywood

Video : Kanwar Matashin Dayasha fiya-fiya akan maryam yahaya shekarar data wuce tace sune sukayiwa jarumar addu’a tafara rashin lafiya.

Kanwar matashin dayasha fiya-fiya saboda maryam yahaya tafito tayi martani zuwa ga jarumar bayan rashin lafiya mai tsawo takama jarumar.

Acikin wani bidiyo wanda budurwar tafitar a shafinta na tiktok wanda zaku gani a kasa👇👇👇 ya jiyo budurwar tanayiwa maryam yahaya allah shi kara tare kuma dacewa tabbas alhakin sune kuma suma sunyi addu’a akan allah yasaka musu na abunda tayiwa dan’uwansu.

Budurwar ta bayyana cewa yayan nata mai suna musa da duka danginta sun tsani jarumar har takai cewa yanzu idan dai har fim da jarumar to basa kallo.

Idan zaku tuna, a shekarar data gabata wani matashi mai suna musa yayi tattaki daga jihar yobe yazo jihar kano domin haduwa da jarumar saboda irin tsananin kaunar dayake mata.

Bayan yazo sai akace masa bata kusa amma yajira a kirata, shikuma yaga bazai iya jiraba, kafin a ankare har yaciro kwalbar fiya-fiya ya kwankwada, nan take yafadi kasa rai a hannun allah.

Bayan yafadi sai aka kira hukumar hisbah suka tafi dashi asibiti, daga baya ansamu da kyar anceto rayuwar matashin inda yanzu haka yana jihar su ta yobe.

Ga cikakken bidiyon wanda muka dakko daga shafin sada bin sulaiman a facebook👇👇👇

Bidiyon kanwar matashin dayasha fiya-fiya akan maryam yahaya

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button