KannywoodLabaran Duniya

Anyiwa uwar gida tsirara bayan an ba hamata iska da dangin amarya

Uwargida ta cakumi ango bayan ya bankade ta a yayin da take nuna isa a gaban amarya

Anyiwa uwar gida tsirara bayan an ba hamata iska da dangin amarya

An jihar naija wani lamari ya afku tsakanin wata uwargida da maigidanta da kuma amarya da danginta wanda ya jawo har ta kai ga an yiwa uwargida tsirara.

A yayin da ake tsakiya da gudanar da shagalin biki na wani bawan Allah a garin Minna ga ke jihar niger, wani lamari ya auku wanda ya ja hankalin munate sosai. Lamarin dai ya fara ne a yayin da uwargida ta ke kokarin nunawa duniya cewa ita ta isa da maigidanta sai ta hau kan cinyarsa ta zauna domin a musu hoto, sai dai kuma shi maigidan nata bai so hakan ba, a sakamakon haka sai kawai ya ture ta har ta fado kasa.

Bayan da Uwargida ta fado kasa sai ta yi kokarin tasowa a yayin da ita kuma amarya ta ke kokarin zuwa jikin angonta sai uwargida ta buge ta a bisa kuskure wanda hakan ya fusata ango  da dangin amarya baki daya. Kamar dai yadda rahoton ya bayyana daga jaridar hausa legit, dangin amarya sun lallasa uwargida sosai wanda har ta kai ga an yaga mata kaya an yi mata tsirara. Sannan kuma rahoton ya cigaba da bayyana yadda ta cakumi maigidan nata ta ci kwalarsa har sai da aka kwaceshi.

Hakikanin Gaskiya wannan lamari ba karamin husuma ya haddasa wa wannan bawan Allah a cikin gidansa domin abunda ya faru din ana ganin shi ne silar da za a samu zamantakewa mai dauke da tsama da kuma gaba da mummunan kishi tsakanin matan guda biyu a cikin gidan auren nasu.

Karanta Lalata da matan kannywood: Sudenly ta kwarewa teema makashi kan batun madigo

Sai dai kuma ana ganin muddin dai maigidan nasu zai zama mai adalci a tsakaninsu, to lallai hakan ba zai zama dalilin wata gaba ko zamantakewa maras dadi ba a tsakaninsu. A yanzu haka dai ana kira ga maigidan da ya kasance mai adalci da kuma jajircewa wurin ganin ya samar da zaman lafiya a cikin gidansa.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button