Labaran Duniya

SUBHANALLAHI : Matar Aure Ta koka Akan Yanda Mijinta Ya korata gida sannan kuma yaki zuwa biko.

“Tunda mijina ya korani Gida Baizo ba kuma ai aiko ba, Nagaji, inaso nasani ko ya hakura dani ko kuma zai mayar dani”inji sakina Lawan A kotu.

Wannan wani Rahoto ne Damuka samo na wasu ma’aurata guda biyu, inda matar take fadawa kotu irin azabar datakesha a gidan mijinta . Sai dai shima mijin yakoka yace matar ce take wahalar dashi.

Wata matar Aure Mai suna, Sakina Lawan, takai karar mijinta,Aliyu isah kotun magajin gari dake kaduna, tana mai roko akan kotun ta tambayi mijinta yana aurenta ko kuma ya daina.

Sakina Ta bayyanawa alkalin Kotu maisuna,Murtala nasir cewa “Tun a watan October ta shekarar 2021 da mijina Aliyu ya korani gida har yau bai neme ni ba,bai aiko ba kuma har yanzu bai fada cewa ya sake niba.

Wannan ne Dalilin Sayasa nakeso kotu ta taimaka ta tursasashi akan ya gayamun matsayi na,saboda babu wanda yasan inda ya dosa”.

Sai dai kuma A nasa Bangaren Mijin nata aliyu, Ya bayyana cewa Wannan maganar duka karya sakina takeyi. Sannan yakara dacewa “Sakina tsigalalliya ce kuma ga rashin kunya,mijin ta bai isa yasata abu tayi ba,haka kuma idan ta tashi Tafiya tawo ba wanda zata fadawa sai dai kawai a nemeta a rasa.

Haka yana daya daga cikin Dalilan dasuka saka na turata gida,domin taje ta jima ko ta kara samun tarbiyya“inji shi.

Sannan Aliyu ya bayyana cewa gyaran gida yakeyi, amma dazarar ya kammala zai dauketa da yayansu su koma sabon gidan su,Sannan kuma a lokacin zai saka yayansa duka a makaranta.

Daga karshe dai alkali malam murtala Nasir, ya dage sahriar zuwa 25 ga wata January, alokacin takoma gida, sannan kuma aliyu yasak yayansa a maranta.

KARANTA : Mijina na neman kasheni da yawan jima’i, Dan allah kotu ta raba aure na dashi- inji wata mata.

RAHOTO : RIGAR YANCI INTERNATIONAL.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button