siyasa

Ganduje Yaci amanata shiyasa wadannan abubuwa suke faruwa dashi : inji kwankwaso.

Tsohon gwamnan jihar kano, sanata rabiu musa kwankwaso yafadi musabbabin rikici tsakanin gwamnan kano, abdullahi umar ganduje dakuma tsagin tsohon gwamnan kano kuma sardaunan kano, Malam ibrahim shekarau.

A wani rahoto da LEGIT.NG HAUSA tafitar ya bayyana cewa, kwankwaso yace rikicin dayake faruwa a jam’iyyar ta APC ta jihar kano bai zo masa da ban mamaki ba,yace dama yasan lokacine kawai amma ko bajima ko badade sai anzo gurin da akazo yanzu.

“Duk wanda yagaza rungumar wanda yayi masa halacci tsawon shekaru,domin shi kansa yasan munyi masa halacci, babu wanda yataba yimasa halaccin danayi masa a siyasa, amma dayasamu dama lokaci daya, sai yakasa jure rike tafiyar kwankwaso da kwankwasiyya”

KARANTA : “Kwankwasiyya ce muke” sabuwar wakar kosan waka mai zafi.

Kwankwaso ya bayyana cewa rikicin dake faruwa a jam’iyyar APC yasamo asaline daga tsantsar son rai dakuma sin zuciya, kwankwaso yakira yanayin da siyasar jihar kano take ciki da sunan “karya fure take bata yaya”.

Hoton kwankwaso da ganduje.(gwamnan jihar kano)

idan zaku tuna a shekarun baya, kwankwaso da ganduje sunyi abokantaka wanda har takai ganduje yayiwa kwankwaso mataimakin gwamna sau biyu na tsawon shekara 8, daga baya rikici yashiga tsakaninsu.

kafin rigimar kwankwaso da ganduje sun kasance abokai kuma aminan juna a siyasa,daga baya siyasa kuma tazo ta rabasu.

1 2Next page

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button