Labaran Duniya

Da dumi-Dumi : Sarkin Kano aminu Ado zai angwance da wata tsohuwar budurwarsa kwanan nan.

Sarkin kano, alhaji aminu ado bayero, na dab da angwancewa da sahibarsa wacce suka dade tare suna soyayya wacce ake kiranta da suna hajiyayye,dake unguwar dorayi a jihar kano.

Jaridar DAILY NIGERIAN HAUSA ta bayyana cewa sarki aminu bayero, wanda matarsa daya dakuma yaya hudu, zai kara aure bayan shafe shekaru kusan talatin da daya da mata daya.

Majiyar Daily Nigerian ta bayyana mata cewa shirye-shirye sunyi nisa tsakanin waliyyan dangin guda biyu,na sarki da kuma na budurwar tasa.

Majiyar takara dacewa baza’ayi wani gagarumin biki ba, saboda aminu ado ba “ba mutum ne mai son fankama ba” sannan kuma itama amaryar danginta ba sanannu bane.

Majiyar tace “sarki yadade suna soyayya da hajiyayye kafin yazama sarki, amma yanzu ankammala shirye-shirye, duk dacewa a baya an daddaga bikin, to dayake ba gagarumin biki za’ayi ba, daga yanzu zuwa kowane lokaci za’a’iya daura auren”.

Anhaifi sarki aminu ado bayero a shekarar 1961 inda a ranar 9 ga watan maris yazama sarki na 15 na kabilar fulani bayan gwamnan kano yatube rawanin tsohon sarkin kano,sanusi lamido bisa wasu dalilai.

Read Also

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button