KannywoodLabaran Duniyasiyasa

Izzar so episode 80 original

Izzar so episode 80 original

Hakikanin gaskiya a cikin shirin izzar so episode 79 Hajiya nafisa ta fara girbar abinda ta shuka. Sai dai kuma alamu sun nuna cewa wannan somin tabi ne, domin ana ganin cewa a izzar so episode 80 ne za ta gane kurenta sosai.

Ga dukkan wanda ya kalli shirin izzar so na yau hakikanin gaskiya sai dai mu ce Allah ya kara basira ga mai bada labarin film din. Mutane da dama na jin dadin yadda shirin ke tafiya musamman ma da aski ya zo gaban goshi. A yanzu dai hajiya izza ta koma gida ba batun zuwa ma’ikata walau karamar walau babbar, wanda hakan ba karamin rasa kima ne a gareta ba.

Cikakken darasi da ke cikin izzar so episode 80

Ga dukkan wanda ya kalli shirin izzar so episode 80 zai gane cewa lallai akwai babban darasi a tattare da shi musamman ma idan an ga yadda makomar hajiya nafisa ta kasance da kuma yadda masu taimaka mata wajen bunne gaskiya tare da kuntatawa masu binta. Haka kuma bayan ganin yadda karshen Nakowa ya kasance da kuma na maigidansa wato Jibrin za mu gane cewa lallai duk wani mai hali irin nasu to ba zai yi karshe mai kyau ba.

Kalli>>maryam yahaya ta saki hotuna ba rigar nono

Haka kuma idan mu ka duba yadda rayuwa ta canzawa masu gaskiya irin su umar hashim da kuma su bada yaji da karima da duk wasu da ke bayan gaskiya, za mu iya gane cewa gaskiya tudun tsira da nasara ne. Domin kuwa duk da irin takurawa da kuma matsin lamba Umar Hashim ya fuskanta amma dayake gaskiya ya rika, kuma ya jajirce tare da yin hakuri a kan gaskiyarsa, sai gashi ya haye kujerar da ake amfani da ita wajen ci masa mutunci.

A daya bangaren kuma munga yadda Rayuwa ta canzawa Karima a yayin da aka lika mata sharri da yin iskanci da nakowa domin a zubar mata da mutunci kuma a tursasa Umar hashim wajen sanya hannu a kan takardar cire kudi ba bisa kaida ba, sai kuma gashi ta zama shugabar ma’aikata a ma’aikatar baki daya.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button