Labaran Duniya

Mijina na neman kasheni da yawan jima’i, Dan allah kotu ta raba aure na dashi- inji wata mata.

wata mata mai yaya uku mai suna,Olamide lawan, ta roki kotun gargajiya mai matakin A a Mapo Ibadan, data kashe aurenta a bisa dalilin cewa mijinta,saheed lawan, yana jima’i da ita har yawuce kima.

A wani rahoto da jaridar DAILY NIGERIAN HAUSA ya bayyana cewa, A karar da olamide ta shigar Ranar juma’a, ta kuma shaidawa kotun cewa mijin nata kuma dan giya ne.

“Shekarar mu 14 kenan da aure na da lawan, dan giya ne da bashi da niyyar dainawa sannan kuma kwata-kwata bashi da tausayi.

“Shi ba abunda yasani illa shan giya,Duka da kuma takura min da jima’i kamar ya kasheni da saduwa,sannan kuma ba ruwansa da yayansa.Gaskiya ni na gaji da zama dashi, ina rokon kotu data taimaka da tara aurenmu”inji ta.

Sannan matar ta kuma roki kotu data hana lawan kiranta a waya, ko kuma zuwa gidan da take.

Sai Dai anashi bangaren,lawan ba haka abun yake ba, inda ya roki kotu akan ta rarrashi olamide domin ta hakura suci gaba da zama tare.

“Na tuba, nayi nadama kuma nadena shan giya,kuma zan cigaba da kula da yayana,zan canza rayuwata”inji lawan wanda tela neshi.

Alkalin kotun, S.M. Akitayo,ya daga zaman sai 3 ga watan maris,sannan, ya shawarci ma’auratan dasu zauna lafiya a tsakaninsu.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button