Labaran Duniya

Wata Sabuwa : bidiyo akan yanda Matan Wani Mutum Suka rabu dashi Saboda yaki ya daina sata.

Akwai bidiyo a can kasa ku danna kansa domin kallon cikakken abunda yafaru.

Rundunar yan sanda a jihar kano, tayi ram da da wani mutum bisa zargin satar babura, bayan yayi yunkurin sace wani babur a karamar hukumar fagge dake cikin garin kano.

Jaridar BBC HAUSA ta ruwaito cewa wani dan sanda ne yakama mutumin mai suna usman zubairu dan shekaru 57 a bakin Bankin UBA dake france road yayin da yake yin kokarin yin gaba da wani babur kirar suzuki.

KARANTA : Yan sanda sun cafke mutumin dayayiwa yara kanana guda 4 fyade yan kasa da shekara 7 a jihar borno.

Dayake gabatar da mutumin a shafinsa na facebook, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar kano, usman ya bayyana cewa yashafe kusan shekaru 10 yana sata, wanda hakan yasa matansa suka guje shi.

“Bani da mata yanzu, saboda sunce bazasu iya zama da barawo ba” inji usman.

Sannan yakara dacewa, asalinsa ba bakano bane, shi dan garin dayi ne, wani gari a jihar katsina, sana’arsa ta satace takaishi garuruwa kamar bauchi,gombe da kano.

Kiyawa yace wannan bashi ne karo na farko da suka kama mai laifin ba, shima kuma ya tabbatar dacewa makonsa shida da fitowa daga gidan yari.

Ga cikakken videon nan akasa ku danna domin ku kalli tattaunawar tasu 👇👇

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button