Labaran Duniya

Kawa ta burmawa aminiyarta wuka a Wuya sanadiyyar cece-kuce

A karamar hukumar kumbotso dake jihar kano, wata kawa ta burmawa kawarta mai suna BAHIJJA wuka a wuya Har saida fa bullo ta makogaronta kamar yanda jaridar ATP HAUSA TV ta wallafa.

Hakan yabiyo bayan wani kashedi da ita bahijjar (wacce aka kashe) takaiwa mahaifiyar kawartata (wacce ta kasheta) na cewa tana jifanta da munanan kalamai a duk lokacin data fito zata tafi makaranta.

A lokacin da Abun yafaru ne aka dauki bahijja aka kaita asibitin murtala, daga nan kuma aka turasu asibitin nasarawa, shigarsu dakin tiyata keda wuya allah ya amshi ranta.

Mahaifiyar bahijja ta bayyana cewa”diyata bahijja tafitane domin zuwa takai karar wata kawarta gurin mahaifiyar domin taja mata kunne sakamakon kiranta dakuma jifanta da kalmar karuwa a duk lokacin data fito zata tafi makaranta, dawowarta da bangani ba kenan sai dai labarin wannan mummunan abu danaji yafaru nayi”

Kakakin rundunar yansandan jihar kano DSP ABDULLAHI HARUNA KIYAWA yace za’a tsaurara bincike sannan a dauki kwakwkwaran mataku akan wannan baiwar allahr wacce ta aikata wannan ta’asa, inda tuni yabada umarni akaita sashin manyan laifuka domin a fadada bincike.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button