Labaran Duniya

DA DUMI-DUMI : Mai bawa Gwamna Ganduje Shawara Tareda Dubban magoya bayansa sun gudu sun koma tsagin shekarau.

SIYASAR KANO : mai baiwa gwamnan kano, Abdullahi umar ganduje shawara akan harkokin jiha,Muhammad shehu, tareda wasu mukarrabansa sun sauya sheka daga tafiyar gidan gwamnatin zuwa tsagin tsohon gwamnan kano, Sanata ibrahim shekarau, bisa wasu dalilai nasu da suka bayyana, wanda aciki suka hada da rashin iya mulki dasukace jam’iyyar tana fuskanta a tsagin gwamnati, karkashin Abdullahi abbas.

Hotunan wasu daga cikin wadanda suka koma tsagin shekarau

Cikin rahoto da jaridar DAILY NIGERIAN tafitar, ya bayyana cewa muhammad shehu yace, zasu marawa tsagin shekarau baya a batun takarar gwamnan kaka mai zuwa, sannan ya kara dacewa mafi yawan al’ummar nasarawa natare dasu, kasancewarsu yansiyasa ne tun daga tushe.

Muhammad shehu yace akwai wasu karin mashawartan suna kan hanya suma domin zuwa su hade da tafiyar gidan malam ibrahim shekarau, karkashin shugabancin ahmad haruna zago,sannan kuma zasu marawa barau jibrin baya a takarar gwamna,a cewarsa kasancewar jama’ar kano ne da kansu suke muradinsa, ba cushe za’a yimusu ba.

Idan zaku tuna a watannin nan dasukawuce akaja zare tsakanin gwamnan kano abdullahi ganduje, da kuma tsagin G7 wanda shekarau ke jagoranta, wanda tuni wasu na jikin gwamna irinsu, farfesa hafizu abubakar, murtala alasan zainawa suka fice daga tsagin gwamnan zuwa tsagin shekarau.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button