KannywoodLabaran Duniya

Zan fito na zagaya gari tsirara idan ba a kula ni ba

A kula ni ko inyi tsirara in shiga kasuwa

A yayin da ake ta fama da tone tonen silili tsakanin jaruman kannywood wanda har ya janyo fallasa batun lalata da mata kafin a saka su a film, a daidai lokacin kuma sai gashi a twitter wata sabuwa ta bulla. An samu wasu maza da kuma mata suna ikirarin Zan fito na zagaya gari tsirara idan ba a kula ni ba. Hakikanin gaskiya wannan batu ya zama ruwan dare a kafafen sada zumunta na zamani musamman ma a wannan lokacin.

Zan fito na zagaya gari tsirara idan ba a kula ni ba
Zan fito na zagaya gari tsirara idan ba a kula ni ba

Wata budurwa mai suna maryam ta bayyana cewa lallai ya zama dole a kula ta idan kuma ba haka ba to za ta fito tsirara za zagaya kasuwa. Wannan dai ikirarin nata ya kasance batu na rashin daraja a matsayinta na budurwa wadda ke neman samun miji a nan gaba. Sai dai kuma ita ko a jikinta ba wani alama na jin kunya ko kadan.

Wannan budurwa dai ta sha raddi kala daban-daban daga followers dinta da kuma wadanda ba followers dinta ba da su ka ci karo da wannan posting nata. Amma kuma ya kamata mu kawo muku wasu daga cikin comments din da aka yi mata domin ku ganewa idanuwan ku, wanda kuma munsan ku ma din ba za ku rasa abin cewa ba.

Zan fito na zagaya gari tsirara idan ba a kula ni ba

Ibrahinisa kawai dariya ya yi ya ce hhh in kin yi tsirarar ma gani ne kawai za a yi ba ci ba. shi kuma MHB cewa ya yi aa me ya yi zafi haka, an kula ki kuma zuwa anjima ma har dm zan miki ayi hira shikenan ko? M.B Tahir kuma cewa ya yi “Waiting for you to arrive at market”. Ma’ana muna jiran isowarki kasuwar.

Zan fito na zagaya gari tsirara idan ba a kula ni ba
Zan fito na zagaya gari tsirara idan ba a kula ni ba

Haka dai mutane su ka cigaba da tofa albarkacin bakinsu a karkashin rubutun da Maryam ta wallafa a shafin ta na twitter dangane da batun fitowa tsira ta je har kasuwa idan har ba a kula ta ba.

Zan fito na zagaya gari tsirara idan ba a kula ni ba
Zan fito na zagaya gari tsirara idan ba a kula ni ba

Shi ma dai pending-ustaz haka ya bishi iska gaba gadi ya yi nasa posting ɗin inda ya ke ikirarin filowa tsirara muddin dai ba a kula shi ba, ba tare da ya san Maryam tana yi ba a daya gefen.

Saboda haka lamarin social media a arewacin Nigeriya ya dauki wani sabon tafarkin da tun farko bai faro da shi ba. Hakikanin gaskiya wannan matsala ce da ya kamata manya da kuma malamai su gaggauta saka baki a cikinta tun kafin lamarin ya yi muni sosai.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button