Uncategorized

Kalaman yabon budurwa

Minene kalaman yabon budurwa?

Kalaman yabon budurwa: Wasu kalamai ne da saurayi ke furtawa budurwa gaba da gaba, ko a waya ko kuma a rubuce domin ya kambama ta ya ya sauya a mata irin yadda ta zama abar bujgewa ga kowa tare da nuna mata yadda ya ke jinta a ransa.

Ya ake furta kalaman yabon budurwa?

A duk lokacin da ya kasance mutum ya kwarewa wata budurwa, babban abinda zai zama banruwa ga shukar soyayyar sa shi ne kalamai. Idan za ka furtawa budurwa kalaman da za ka yabeta sai ka yi amfani da kalamai masu ɗauke ta abubuwan jan hankali kamar haka:

Ya ke masoyiyata, hakikanin gaskiya na yi babbar Sa’a da na sameni. Domin kuwa a wannan zamanin ba samun budurwa ne ke da wuya ba, a’a samun budurwa ta gari mai kamun kai wadda ta kasance ana koyi da kyawawan halayenta shi ne aiki.

Sai kuma gashi Ni Ubangiji ya haɗa ni da kyakkyawar da ta haɗa komai, tun daga kyawun hali da kyawun sura da cikar halitta. Bugu da kari kuma ga cikakken asali da ya kasance kowa na burin ganin ya hada zuri’a da dangin mutunci irin naku.

Hakikanin gaskiya ko dan wannan dole na yiwa Ubangiji godiya da ya mallaka min ke, domin nasan Ni na gama samun babban rabo, sai dai kawai na jira lahirarmu ta yi kyau.

Karanta>>https://hausanovels.org/kalaman-bada-hakuri-a-soyayya/

Conclusion:

Kun ga a nan mun yi amfani da wasu kalamai da su ka kasance na kambamawa da kuma yabo wanda zai sa budurwar ta ji dadin gaske a cikin zuciyar ta, ta yadda Soyayyar da ta ke yi wa saurayin ta karu sosai a zuciyarta.

A saboda haka, idan mutum zai furta kalaman soyayya wa budurwa, yana da kyau ya kula da abinda zai fada mata ba tare da ya yi karin gishiri ta yadda har zata ji a ranta cewa karya kawai ya ke sharar mata.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button