Kalaman Soyayya

sabbin zafafan kalaman soyayya 2022

Minene kalaman soyayya?

Mutane da yawa na son yin soyayya amma bayan komai ya saitu a rayuwarsu da abokan soyayyar su sai abubuwa su canza. Ba komai ne ke kawo haka ba face rashin iya tafiyar da soyayyar ta hanyar da ta dace. Babban abinda ya kamata masoya su nakalta shi ne yadda za su saita tafiyar soyayyarsu ta hanyar kalamai. A saboda haka ne ma ya sa mu ka kawo muku sabbin zafafan kalaman soyayya 2022.

sabbin zafafan kalaman soyayya

ya ake furta kalaman soyayya?

A duk lokacin da ka ke muradin farantawa abokin soyayyarka rai, kana bukatar amfani da salo daban daban da zai ja hankalin wanda ka ke so. A cikin hanyoyin da ake bi domin cimma wannan muradin kuwa akwai furta kalaman soyayya. Sai dai mutane da dama basu san yadda za su furta wannan kalaman na soyayya ta yadda za su sace zuciyar wanda su ke so ba.

Saboda haka ne ma mu ka ga ya kamata mu kawo muku irin yadda ya kamata mu furta sabbin kalaman soyayya da za su sa mu farantawa masoyan mu rai. Salon da ake amfani da shi wajen furta kalaman soyayya ya hada da furta kalaman soyayya masu ratsa zuciya, kalaman soyayya masu dadi, da sauran su.

sabbin zafafan kalaman soyayya 2022

sabbin zafafan kalaman soyayya  2022

Na mata: Ya kai shalele na, a duk lokacin da na tuna ka a cikin zuciyata, nakan ji wani farin ciki wanda ya kasance na daban da irin sauran farin cikin da na saba ji a dukkan sauran lokuta.  Wannan ne dalilin da ya sa na fahimci kai na daban ne a cikin duniyata.

Ka sani cewa ina sonka, irin son da tsarkakakkiyar zuciya ke yi a yayin da ta fada kogin kauna. Rokon da zan yi a gareka shi ne, samun soyayya ta gaskiya wadda babu wani sirki ko kadan a cikinta. Soyayyar da cikin zuciya ya fi kyau fiye da wajenta, ma’ana yadda a ke so na a cikin zuciyarka ya dara yadda na fahimci kana so na a zahiri.

Na maza: Shalele na, hakiki ke kyakkyawa ce da kyawunki ya kai kololuwa ta yadda ko mata yan uwanki su ka kalla sai sun yaba. Hakika samunki a wurina babban rabo ne, duk da cewa akwai mata da yawa da zan iya samu amma ba kamar ki ba.

Baby na, ina fatan za ki kasance mai bani tsaftatacciyar soyayya da zai kasance ko da a bayan ido na ne za ki nunawa duniya matsayina a cikin zuciyarki fiye da yadda za ki nuna a gabana. Abinda na e nufi a nan shi ne, ki kasance kina min soyayya irin wadda matan aljanna ke yiwa mazajen su.

karantahttps://hausanovels.org/kalaman-soyayya-masu-tsuma-zuciya/

Wannan soyayya ita ce wadda ta kasance soyayya ta gaskiya wadda babu wani sirki a cikinta sai tsabar gaskiya da rikon amana. Hakika idan ki ka bani irin wannan soyayyar, nima na yi alkawarin baki tawa irinta kuma Allah ne shaida domin shi ne yasan cikin zuciyata. za ku iya sauraran wadannan kalaman soyayyar da kunnuwanku.

Gargadi:

Wannan kalaman dole ne kafin namiji ko mace ta furta su sai kun tsarkake zuciyarku  da so na gaskiya, sannan kuma kun nisanta yaudara da cin amana daga zukatanku. Idan kun lura munyi amfani da wasu kalmomi wanda idan dan yaurada ko yar yaudara su ka yi amfani da su, to tabbas Ubangiji ba zai bar su tafi haka nan ba sai ya hukunta su bisa hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button