Labaran Duniya

YAN SANDA SUN KUBUTAR DA JAKIN DA AKAYI GARKUWA DASHI A JIHAR KATSINA

Wani Jaki A Jihar Katsina Yashaki iskar yanci bayan da Rundunar yan sandan jihar suka kubutar dashi daga hannun Yan fashin Daji Dasukayi Garkuwa Dashi A jihar Katsina.

Rahoton Jaridar Daily Nigerian hausa ya bayyana cewa kakakin Rundunar yan sandan jihar, IGP Gambo isah ya tabbatar da Kubutar Da jakin, tare da Sauran dabbobin gida da Dama,Yafadi hakan a yayin da yake bayanin irin nasarar Da Rundunar ta samu a shekarar 2021.

A cewarsa Rundunar ta kwato dabbobi 1,243 wadandan suka hada da shanu guda 867, da kuma tumaki 352 da awaki 24 sai kuma shi wannan jakin.

Sp isah ya kara dacewa yan ta’adda na amfani da jakin wurin tafiye-Tafiye, inda yace suna dorawa jakin kaya, matansu ko kuma yayansu idan zasuyi bakaguro.

“Jaki na mutanen gari ne, idan yan ta’adda sukazo satar dabbobi sai su hada dashi sukada sutafi,domin suna amfani dashi”inji IGP isah

Akalla sun bayyana cewa sun kama masu laifi 999 a shekarar data gabata a jihar, sannan kuma sun bindigogi da alburusai da dama.

sannan kakakin yayiwa al’ummar jihar Katsina dama na sauran kasa baki daya albishir nacewa acikin wannan sabuwar shekarar zasu ga ingancin tsaro sosai.

yace gwamnatin tarayya zata samar da sabbin kayan aiki hadi da kuma daukar sabbin jami’an yan sanda da kuma amfani da hanyoyin sadarwa gurin maganin yan ta’adda da sauransu.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button