KannywoodLabaran Duniya

Madagwal: ana lalata da mata kafin a saka su a Film a kannywood

Madagwal: Yadda ake yin lalata da mata kafin saka su a film

A yayin da wani sabon abin rikici ya kara budewa a masana’antar kannywood, jaruman cikinta na kara zarge dantse wajen tonawa junansu asiri. Tun lokacin da ladin chima ta tattauna da BBC Hausa ta shaida musu cewa ana biyan ta dubu biyu idan an sakata a fim, tun a lokacin ne dai rikici ya Kunno Kai a kannywood.

Bayan Nasiru Sarkin Waka ya fito ya bayyana cewa lallai ana neman mata kafin a saka su a Film, to gashi Ali Artwork ma ya fito ya bayyana wa duniya cewa lallai batun gaskiya ne ana neman mata kafin a saka su a Film.

Asirin kannywood da Ali Artwork ya tona

Madagwal dai kamar yadda kowa ya sani shi ma yana daga cikin jaruman da su ke da kusanci da manya a cikin masana’antar kannywood, a saboda shi ma ya san sirruka da dama.

Madagwal dai ya bayyana cewa lallai batun bada kai da mata su ke yi kafin a saka su a Film ba zargi ba ne, gaskiya ne. Ya cigaba da bayyana cewa jarumai irin su Ali Nuhu ya kamata su ke jin tsoron Allahdomin kuwa su ne manya kuma sun san komai a wannan harkar.

Madagwal ya kuma yabawa zakakurin jarumi wato Nasiru Sarkin waka sakamakon fitowa da ya yi ya fadi gaskiya ba tare da wani tsoro ba. A cewar sa, mafi yawan jarumai sun san gaskiyar abinda ke faruwa a cikin masana’antar kannywood amma saboda tsoro basa iya fitowa su fadi gaskiya. Jarumin ya yiwa Nasiru Sarkin waka fatan samun kariya daga dukkan wani sharri da kuma tuggun makiya.

Kalli bidiyon

 

Batun gaskiya kan yadda ake biyan yan wasu kuɗin aikinsu a kannywood

Har wa yau Ali Artwork ba a iya batun fasikanci da mata kafin a saka su a Film ya tsaya ba, domin kuwa ya tabo bangaren yadda ake sallamar jarumai hakkin su bayan an kammala shooting.

A wannan bangaren ma jarumin ya bayyana irin yadda ake zaluntar yan wasa a yayin da ake biris da su bayan an je an wuni cikin rana ga yunwa ga kishirwa. Ya ce wani lokacin ma sai dai idan kana da kudi a aljihunka ka nemi abinci, ina kuma baka da su to ta ƙare maka.

Haka kuma ya kara bayyana cewa, hatta da kuɗin aikin ka wani lokacin sai su gagara duk da cewa producers na zabtare kuɗin da ake basu domin su sallami yan wasan. Wannan batu kuwa ya kasance tabbatacce a yayin da wasu jaruman ma ke rasa kuɗin motar komawa gida bayan an dawo daga location saboda an ki a biyasu kudin aikin su.

martanin Aminu s bono ga ladin chima ya hargitsa kannywood

Jarumin har ya bada misalin yadda abun ya faru a kansa wani lokaci da Ali Nuhu ya kirashi ya je Kaduna domin yi musu editing na wani Film mai suna namiji kanen ajali. A wannan lokacin ya bayyana cewa bai da ya kwashe sama da sati 2 yana musu aiki ko sisi ba a bashi ba, sannan kuma daga bisani ma ta aka saka Film ɗin a kasuwa hakkin sa bai zo hannun saba.

Ya ce a sakamakon haka ne ya je ya sami Ali Nuhu domin a biyasu kudin aikinsa da su ka kai 100k, dubu ɗari amma dakyar ya samu aka bashi dubu arba’in shi ma sai da rai ya ɓaci. Ya ce tun daga wannan lokacin ne Ali Nuhu ya daina nemansa a duk wani aiki da ya taso, karshe ma har Umar m sharif ya taba kiransa domin ya yi musu aikin wani Film amma da Ali Nuhu ya ji labari nan take ya kira shi ya ce ba za a bashi aikin ba, wanda kuma har yau babu shiri a tsakanin su.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button