Labaran Duniya

Innalillahi wa’innailaihi raji’un: Ankama wani mahaifi mai shekaru 65 da laifin yiwa yarsa mai shekaru 17 fyade.

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya NSCDC a jihar OGUN, ta gurfanar da wani magidancin mutum mai suna,Rojaiye Balogun, Da laifin yiwa diyarsa (ansakaya sunanta) mai shekaru 17 fyade.

Da yake gabatar da wanda ake zargi a hedikwatar hukumar NSCDC dake Abeokuta babban birnin jihar ogun, mista kolawole taiwo,Kwamandan Rundunar NSCDC na jihar, ya bayyana cewa wani nakusa da yarinyar ne yakai rahoto sashin yaki da fataucin bil’adama na rundunar yan sandan jihar.

Mista Taiwo ya bayyana cewa lamarin yafaru ne a imomo-ijobu dake karamar hukumar ijebu ta arewa maso gabas a jihar ta ogun, kamar yanda rahoton ya bayyana.

Yakara dacewa wanda ake zargin ya amsa laifunsa, inda ya bayyana cewa sharrin shaidan ne yasashi yin lalata da yarinyar mai shekaru 17.

KARANTA : Mijina yana barazanar kashe ni da yayana

Kazalika yakara dacewa zasu cigaba da bincikar al’amarin, muddin aka tabbatar da faruwar hakan, zasu gurfanar dashi agaban kotu domin yagirbi abunda ya shuka.

Balogun, wanda ya aikata laifin yace yayi nadamar abunda ya aikata, ya bayyana cewa wacce yayiwa aika-aikar ba diyarsa bace , yace mahaifiyarta ce takawota gidansa tun tana yar shekara 10, sannan yace sau daya yayi lalata da ita,lokacin da mahaifiyarta ta fita unguwa.

KARANTA : An yankewa Malami hukuncin Daurin Rai da rai a gidan kaso bisa laifin yiwa yarinya yar shekara 5 fyade.

Da take magana da yan jarida wacce iftila’in ya fadawa, ta bayyana cewa karya mutumin yakeyi, sau hudu yana lalata da ita, takara dacewa karya yakeyi cewa shi ba mahaifinta bane.

Jaridar DIMOKURADIYYA ta ruwaito cewa wanda lamarin yashafa tace na karshe da yayi amfani da ita yayi mata alkawarin bata naira 1000 domin ya kwanta da ita, amma taki, a lokacin ne ya kwanta da ita ta karfi.Tace ta kaiwa mahaifiyarta kara amma da ita ba.

Zaku iya ajiye mana ra’ayoyinku ta hanyar yimana comments a akwatin dake kasa 👇👇

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button