Labaran Duniya

KADDARA : Kotu ta daure Matashi a gidan yari Sakamakon satar Talo-Talo A kano.

Kotun Shari’ar musulunci a kano ta daure matashi Dan shekaru 23 mai suna,Nura Usman, Hukuncin daurin Watanni biyu a gidan kaso bisa kamashi da laifin satar talo-talo.

Matashin wanda mazaunin unguwar rimin kebe quarters ne dake kano,an yanke masa hukuncin ne bayan ya amsa laifinsa.

Alkalin kotun,Mansur Ibrahim ya kuma bashi zabin biyan tarar kudi naira 20,000 sannan kuma ya biya mai talo-talon diyyar kudi naira 1,6000.

Tun da farko dai lauyan masu shigar da kara,abdullahi Muhammed ya shaidawa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin a ranar 1 ga watan January na sabuwar shekarar 2022 a unguwar rimin kebe dake kano.

yace wanda ake tuhumar ya kutsa kai cikin gidan mai karar inda yasaci talo-talo guda daya, sai dai kuma wanda ake tuhuma ya sayar da Talo-Talon akan kudi naira 7000.

lauya abdullahi Muhammad ya bayyana cewa hakan yaci karo da tanadin sashe na 133 na dokar shari’ar jihar kano.

KADDARA : Kotu ta daure Matashi a gidan yari Sakamakon satar Talo-Talo A kano.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button