Labaran Duniya

Duniya ina zaki damu: wata uwa ta siyar da jaririnta naira 150,000.

Wata mata mai shekaru 23 ta amsa laifinta na siyarda jaririnta dan wata uku akan kudi naira dubu dari da hamsin (150,000).

Matar mai suna, mercy okoh, ta bayyanawa kamfanin dillancin labarai na vanguard cewa,kuncin rayuwa, fatara da talauci sune suka addabeta har hakan takaita ga siyar da jaririn na ta domin tasamu kudin dazata biya kudin haya dakuma al’amuran yauda kullum.

Mahaifiyar yaron ta bayyana cewa ,mahaifin yaron yagujeta a lokacin da take dauke da cikin yaron wata shida, kuma tanada sauran yara biyu da tabarsu a wurin mahaifiyarta take kula dasu tun bayan data haifi jaririn, wanda haihuwar yaron ne tasa ta daina abincin siyarwa datake, dama acewarta dashi ta dogara.

Tace” Bantaba aikata irin wannan mummunan aiki ba,jaririna danasiyar naira 150,000 na aikata hakanne domin nasamu kudin dazan biya kudin haya dama sauran abubuwa, domin kullum cikin kuncin rayuwa nake,damuwa tana cin raina”.

“Mijina yaguje ni bayan wata shida da samun cikin jaririn, bani da wani zabi banda wannan nasiyarda jaririn,amma mutumin daya hadani da mai sayen jaririn yace dan’uwansa yanaso ya aureni”.

Ta kara da cewa” a lokacin danake kokarin mika jaririn nawa mai wata uku bayan anbani kudin, a wannan halin jami’an yan sanda suka shigo lamarin suka kamani”.

Daga karshe jaridar vanguard ta ruwaito cewa, yanzu haka jami’an yan sanda sun baza komarsu domin kamo sauran masu laifin.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button