Kannywood

Tofa! kalli yadda rahma sadau ta yi shigar tsiraici a cikin film din indiya

Tofa! kalli yadda rahma sadau ta yi shigar tsiraici a cikin film din indiya

Tofa! kalli yadda rahma sadau ta yi shigar tsiraici a cikin film din indiya

Shigar tsiraici a kasar hausa wani abu ne da ya kasance abin kyama kuma abin kunya da duk matar da aka gani tana yi sai an dauketa lalatacciya kuma yar iska. Bayan cika da tumbatsa da fitacciyar jarumar finafinan kannywood wato rahma sadau ta yi, sai ta yi tsallen badake daga wannan masana’antar ta kannywood zuwa wata masana’antar ta daban.

Rahma Sadau dai ta garzaya ne zuwa masana’antar bollywood da ke kasar India domin tana da burin taka rawar gani har a indiyan film bayan takawar da ta yi a kannywood. Sai dai kuma abinda aka yi hasashen zai taka mata burki a waccan masana’antar shi ne yanayin shigar su da kuma al-adun rungumar mace ba tare da jin komai da.

A bisa mamaki kuma sai ga shi rahma sadau ta yi shiga irin ta yan indiya din ba tare da ta ji komai a jikinta ba, hakan kuma ba karamin mamaki ya baiwa mutanen arewacin nigeria da duk inda wasu hausawa su ke a nahiyar duniya ba.

Ita dai rahma sadau ta sha yin abubuwan da ke zame mata abin surutu a cikin al-umma, sai dai kuma ita bata dauki abin surutu a matsayin wani abu ba face hanyar samun karin suna kamar yadda wani mutum ya fada.

Inda Rahma Sadau ta yi shigar tsiraici

A yanzu haka dai rahma sadau na cigaba da kokarinta a cikin film din nasu mai suna khudaa hafiz da za su saki a nan gaba wanda kuma ake ganin shi ne film na farko da aka samu wata jaruma daga masanaantar kannywood ta fito a cikinsa a indiya din. Haka kuma rahama sadau za ta aje wani tarihi da za a ce kaf kannywood babu wani jarumin da ya ajje irinsa cikin maza ko mata duk da dai an taba samun jarumi isa feruzkhan ya taba yin bidiyon waka da jarumar indiya din.

za ku iya kallon bidiyoyi da su ka shafi wanna a tashar mu ta youtube mai suna Asusu Tv

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button