Saturday, 25 September, 2021

Ads Banner

Babban Dan ganduje yamaka babarsa gwaggo a kotu sakamakon zarginta da amundahana dakuma azurta kanta .


Babban dan gwamnan kano,Abdul-aziz ganduje, yamaka mahaifiyarsa hafsat ganduje a gaban hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC akan zarginta da almundahana dakuma azurta kanta ta hanyar da bata dace ba.

Tuni hukumar EFCC Ta aikawa da Hafsat ganduje da takardar goron gayyata domin ta amsa tambayoyi amma Taki amsa gayyatar, bakuma ta bayar da wani uzuri akarance ko arubuce ba kamar yanda Jaridar DAILY NIGERIAN HAUSA Ta wallafa

Abubuwan da wasikar Abdul-aziz ta kunsa sun hada da badakalar filaye Da kuma Kudade. Sai dai kuma kakain hukumar ta EFCC, wilson uwurajen yaki cewa komai game da batun da akayi masa tambaya akai.

Idan ba’a manta ba dama a baya anzargi Gwamnan kano dr abdullahi ganduje da yin badakala ta dalar amurka sama da miliyan biyar,inda aka nunosa awani bidiyo yana sunkuma sinki sinkin daloli yana durawa a babbar riga,sai dai kuma gwamnan yakaryata wannan videon tareda kai karar jaridar DAILY NIGERIAN tareda mawallafinta jaafar jaafar gaban kotu game da batun dollars din.

Rahoto daga DAILY NIGERIAN HAUSA

One comment on “Babban Dan ganduje yamaka babarsa gwaggo a kotu sakamakon zarginta da amundahana dakuma azurta kanta .

Mukhtar nuhu sulaiman

Thank you

Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *