Friday, 03 December, 2021

Mawaki Rarara zai tsaya takarar Dan majalisa a katsina


Babban mawakin siyasa a arewacin najeriya, dauda kahutu, wanda akafi sani da RARARA, ya bayyana cewa maganar da aketa yadawa tacewa zai fito takarar dan majalisar wakilai ta  tarayya mai wakiltar karamar hukumar bakori da danja gaskiyane.

 

Mujallar fim ta bayyana cewa Rarara ne ya tabbatar mata da haka a wata hira datayi dashi.

 

Mawakin yace kwanannan zai tsunduma yawo jihohin najeriya domin nuna musu ayyukan cigaban da buhari yayi.

 

Yace “idan na kammala wannan aikin dake gabana,to zan tsaya takarar dan majalisar jiha dake wakiltar bakori da danja, idan kuma wannan aikin yasha gabana,sai kuma aduba batun nan gaba.

One comment on “Mawaki Rarara zai tsaya takarar Dan majalisa a katsina

[…] KARANTA : Mawaki Rarara zai tsaya takarar Dan majalisa a katsina […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *