Saturday, 25 September, 2021

Ads Banner

Mai kanti ya ragargaji yan daba biyu bayan dasukayin kokarin shiga shagonsa suyi sata


Wani mai kanti dake jihar adamawa yayi jarumtar taran wadansu yan shila (matasan samari yan daba) dasuka yi kokarin shiga shagonsa domin suyi sata.

Wadanda ake zargin sune, umar sa’ad mai shekaru 18 sai kuma da mohammed idris mai shekaru 20,sun lallaba shagon mutumin da misalin karfe 2:00 na dare a ranar 2 September 2021 da addunansu,guduma,sanduna dakuma sauran muggan makamai kamar yanda LIB ta wallafa.

Isar su shagon keda wuya suka hau kofar da sara da zummar su fasata ta karfi dayaji.

Suna kici-kicin balle shagonne mai kantin yajiyo kara yafito.

Cikin sauri mai kantin mai suna Muhammad yafito da addarsa ya lallabo domin ya iso wurin.

Dasuka hangoshi sai daya daga cikinsu ya gudu, dayan kuma saboda karfin hali irinna dan daba saiya dauki adda yatunkari mai shagon kamar yanda LIB ta wallafa.

Mai kantin yasamu nasarar sharbawa dan daban adda a hannunsa na hagu yayinda shikuma dan daban yasare shi wanda hakan yakaishi ga zubarda jini har yafita daga hayyacinsa.

Yayin da dan daban yaga jini yana zuba a jikin mai shagon saiya gudu, domin a zatonsa ya kasheshi ne.

Bayan jin hayaniyar ne yan’uwan mai shagon suka fito daga cikin gida da sauri suka daukeshi zuwa asibiti.

Washe gari yansanda sukabi sawun jini har gidan wanda ake zargi dake unguwar sanga bode kuma aka sami nasarar kamashi shida abokin harkar tasa.

Angabatar dasu a gaban kotun majistire dake yola a ranar 10 September 2021 saboda zarginsu da aiwatar da ta’addanci,balle wurin da ake ajje dukiya dakuma dakuma cutar da wani bisa ganganci, nan take suka amsa laifukansu.

Bayan amsa laifukansu, alkalin kotun, aliyu bawuro ya dage karar zuwa 23 September 2021 domin tabbatar da wasu shaidu sannan yayi umarnin a ajiyesu a gidan gyaran hali inji jaridar Legit.hausa.ng

0 comments on “Mai kanti ya ragargaji yan daba biyu bayan dasukayin kokarin shiga shagonsa suyi sata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *