Saturday, 25 September, 2021

Ads Banner

Wani hamshakin dan kasuwa A kano Yayiwa diyar makocinsa mai shekaru 14 fyade a kano


Wani hamshakin dan kasuwa a kano mai suna,alhaji ibrahim wanda yake zaune a unguwar agadasawa yayiwa diyar makocinsa ciki ta hanyar fyade,yarinyar mi suna humaira mai shekaru 14 tana makarantar gaba da sakandire aji 3 (JSS3)

Jaridar HAUSA DAILY TIMES Taruwaito cewa mujallar neptune prime ce ta zanta da yarinyar kuma yarinyar ta shaida musu abunda yafaru tana mai cewa”Alhaji ibrahim yakirani zuwa gidansa wata rana tareda cewa nazo zai aikeni, lokacin da mukashiga gidan sai naga iyalinsa basa nan, ma’ana bakowa agidan,ya kulle kofa sannan ya bani lemo tareda yimin barazanar idan banshaba zai kasheni.

Na karbi lemon nasha, gamashan lemon keda wuya sai naji gabadaya kasala ta kamani, ta haka yasamu dam yamin fyade”.

Humaira takara dacewa tun daga sannan saudaya taga jinin al’adarta, bayan wasu watanni sai ta sanar da mahaifinta,take mahifinnata mai suna,hussaini ado ya dauketa zuwa aaibiti, bayan asibiti sunyi gwaje-gwaje sai suka fadawa mahaifinta cewa yanemi kayan haihuwa domin lokacin haihuwarta yakusa.

Mahaifiyar yarinyar mai suna, hajiya rafa’atu hussaini tayi wa majiyar Hausa daily times bayanin cewa bata taba zargin cewar yar tata nada cikiba har saida ta haihu,kuma ta tabbatar musu da cewa makobcinsu alhaji ibrahim shiyayi mata cikin.

Sai dai a bangaren alhaji ibrahim bayan antunkareshi da maganar saiya musa, kuma yace aje ayi gwajin kwayar halitta na DNA, bayan aje anyi likitan yatabbatar dacewa lallai dan nasa ne, amma kuma alaji ibrahim din bai yarda ba yasake cewa aje wani asibitin.

Tuni dai iyayen Yarinyar suka shigar da kara gaban yan sanda, bayan shigar dakarar kuma sai iyayen yarinyar suka rasa inda karar ta dosa sakamakon anki ayi bincike, kuma maganar tana nema ta shashance, iyayen yarinyar dai suna zargin alaji ibrahim ne yake nema yayi amfani da dukiyarsa domin shashantar da lamarin.

Iyayen humaira sun nemi taimakon kungiyoyin kare hakkin dan adam da kuma hukumar hisbah na jihar kano dama wasu manya-manyan kungiyoyo domin su shiga cikin maganar kamar yanda HAUSA DAILY TIMES Ta ruwaito.

0 comments on “Wani hamshakin dan kasuwa A kano Yayiwa diyar makocinsa mai shekaru 14 fyade a kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *