siyasa

MATSAYINMU A JAM’IYAR APC TA JIHAR KANO -SHEKARAU.

Tsohon gwamnan jihar kano,sardaunan kano, sanata Malam ibrahim shekarau, ya bayyana wani sako a safiyar yau laraba 20 ga watan october 2021 a shafinsa na dandalin sada zumunta na facebook,inda ya bayyana matsayarsa a jam’iyar Apc a kano.

Sanata ibrahim shekarau yayi bayani da a game da abubuwa da dama, ku karanta anan kasa ga sakon nasa kamar haka.

“Assalamu alaikum.

Da farko ina amfani da wannan lokaci nataya duk al’ummar musulmi farincikin zagayowar ranar da aka haifi manzon allah s a w, wacce gwamnatin tarayya a jiya taware a matsayin rana ta musamman don tunawa da ita”.

“Annabi muhammad s a w shine mafi kaunar mu a duniya,bayan allah damuke shaukin samun cetonsa a lahira,halitta kebantacciya a gurin allah muke koyi da ita,allah yakarawa manzon allah s a w daraja da wasila fil jannati”.

“Haka kuma ina amfani da wannan dama na sanarda yan’uwa da dangi na siyasa da masoya a ko ina dangane da halin da jam’iyarmu ta APC ke ciki a jihar kano”.

“Ni sanata ibrahim shekarau, na jagoranci wasu daga cikin mutanen da aka zabemu daga majalisar kasa,mun shigar da kuka ga uwar jam’iya akan rashin gudanar da abubuwan dasuka shafi jam’iya tare damu, muzababbu ne, jama’armu suna da hakki, an karbi korafinmu da mutuntawa, mungode, muna fatan warware takaddamar cikin lumana”.

“Ina sanar da duk jama’armu cewa ina cikin jam’iyar APC DARAM-DAM,zamu tsaya har illa masha allah, a wannan tafiya tamu babu cin mutunci babu zagi babu wulakanta wani,munyi hakuri amma bazamu lamunci sakarci ba.korafinmu yana gaban mahukunta.Bazamu saurari kowa ba sai wandanda muka kai musu kuka”.

“A jihar kano alhaji ahmadu haruna zago shine shugaban jam’iyya zababbe a wurinmu,munayi masa addu’ar allah ya karfafi zuciyarsa kuma allah yatayashi riko, sauran wadanda aka zabesu tare dashi su 35 muna rokon allah yayi musu jagora”.

“Allah yataimaki najeriya.

Allah ya taimaki jihar kano.

Allah yataimaki jam’iyarmu ta APC.

Allah yayi riko da hannun shugabanninmu.

Alkah yabamu lafiya da zama lafiya.

Nagode.

MSI

Sanata ibrahim shekarau.

Sardaunan kano”.

Wannan shine sakon da sanata ibrahim shekarau ya wallafa a shafinsa na facebook.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button