siyasa

DA DUMI-DUMI : UWAR JAM’IYAR APC TA KASA TA WATSAWA SHEKARAU KASA A IDO TACE ZABEN ABDULLAHI ABBAS KADAI TASANI.

A wani rahoto dayake zuwar mana yanzu-yanzu, uwar jam’iyar APC ta kasa tace batasan anyi zabe biyu a kano ba, tace zaben abdullahi abbas kadai tasan anyi kuma shiya cinye.

Mambobin kwamitin da uwar jam’iyar APC ta kasa ta aika kano domin sulhunta yayan jam’iyar tuni sun dira har sun fara aiki.

KARANTA NAN:APC :ZABEN ABDULLAHI ABBAS YA JANYOWA JAMI’IN DAN SANDA ALAKAKAI HAR TAKAI GA BINCIKE.

Mutane Da dama sun yi tunanin cewa wannan sulhu za’a yishi tsakanin Bangaren malam shekarau da kuma na ganduje.

Sai dai kuma daga dirar jami’an kwamitin, sai shugaban kwamitin,tony macfoy ya bayyana cewa korafe-korafen kan zaben da akayi a dakin taron filin sani abacha, wanda abdullahi abbas yayi nasara kawai zasu saurara.

KARANTA NAN:Saura kadan na fasa kwai kowa yasan abunda yake faruwa-muhuyi magaji

Shugaban kwamitin yace, uwar jam’iyar zabe daya tasan anyi a kano, kuma shine tsagin gwamnati wanda abdullahi abbas yayi nasara.

Yayin bayanin ya bayyana cewa kwamitin zai zauna tsawon kwanaki 3, daga yau asabar zuwa ranar litinin, daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma a sakateriyar jam’iyar dake kano.

KARANTA NAN:Yanzu-yanzu: Ganduje yasauke mu’az magaji dan sarauniya daga mukaminsa a karo na biyu.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button