Tuesday, 26 October, 2021

Ads Banner

Yanzu-yanzu; Kotu ta kori mai mala buni daga matsayin shugaban riko na jam’iyar APC sannan ta dakatar da taron karamar hukuma.


Wata babbar kotu dake Asaba,babban birnin jihar delta dake najeriya, ta dakatar da taron da jam’yar APC Mai mulki ta shirya ta gabatar na kananan hukumomi a ranar 4 ga oktoban 2021.

Jaridar DAILY TRUST ta ruwaito cewa kotun ta hana gwamnan jihar yobe,mai mala buni, cigaba da daukar kansa a matsayin shugaban riko na jam’iyar ta APC Har sai ta yanke hukunci.

Kotun ta bayar da umarnin ne bayan da wasu fusatattun jiga-jigan jam’iyar ta APC suka shigar da kara gabanta.

A cewar THE GUARDIAN , mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Olorogun Elvis Ayomanor, wanda ya jagoranci wasu jami’an jam’iyyar APC na Delta, ya garzaya kotu biyo bayan babban taron mazabu na ranar 10 ga watan Yuli, 2021, wanda ake zargin an janye.

0 comments on “Yanzu-yanzu; Kotu ta kori mai mala buni daga matsayin shugaban riko na jam’iyar APC sannan ta dakatar da taron karamar hukuma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *