Friday, 24 September, 2021

Ads Banner

Za’a kama sheikh Aminu Daurawa A dalilin shirin Tambaya Mabudin Ilimi.


Hukumar kare hakkin mallaka ta kasa (copyright commission) ta aikawa da fitaccen malamin addinin musulunci,sheikh aminu ibrahim daurawa da takardar gayyata bisa zarginsa dayin shirin tambaya mabudin ilimi ba bisa ka’ida ba.

Hukumar tace tana bukatar sheikh daurawa yazo da kansa ranar laraba ko kuma su sa a kamosa ta hannun kwamishinan yan sanda.

A jiya talata ne sheikh aminu daurawa ya aika lauyoyinsa gurin hukumar kare hakkin mallaka ta kasa (copyright commission) domin suyi bayani a gameda shirinna tambaya mabudin ilimi.a cikin bayanin da lauyoyin sukayi sunce a shirye suke su zauna da gwamnatin tarayya lafiya.

Sheikh Aminu daurawa ya aikawa hukumar da takardunne domin ya tabbatar mata da cewa shirin tambaya mabudin ilimi shirinasane kuma iliminsane,amma kuma batareda yakawo wata takarda datake bayyana cewa shirinna tambaya mabudin ilimi mallakinsane ba.

Bayan da aka gabatar da wadannan takardu da sheikh aminu daurawa ya aika lauyoyinsa sukai hukumar kare hakkin mallaka ta kasa (copyright commission), nan take sukace bayanan da sheikh aminu daurawa ya bayar basu gamsar dasu ba, saboda haka suka turawa sheikh aminu daurawa takarda akan cewa suna bukatar ganinsa a ranar laraba domin yabasu gamsassun hujjoji, idan kuma bai zoba zasu bawa kwamishinan yansanda umarni domin akamasa.

0 comments on “Za’a kama sheikh Aminu Daurawa A dalilin shirin Tambaya Mabudin Ilimi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *