Tuesday, 26 October, 2021

Ads Banner

Anraba Takardun Gargadi Akan Kar a Sake Zaben Jam’iyar APC a Kaduna


Anraba takardu a wasu masallatai na jihar kaduna, inda acikin takardun ake gargadin mutane da kada su sake sukara zaben jam’iyar APC a fadin jihar.

Ana zargin cewa raba takardun nada alaka da zaben kananan hukumomi dake tunkarowa a yanzu haka.

Wadanda suka rubuta takardun sun kawo dalilan abinda yasa sukace kar asake zabar jam’iyar ta APC.

Ga kadan daga cikin dalilan nasu;

APC ta kori ma’aikata

APC ta rushe kasuwanni.

APC ta lalata tsaro.

APC ta hana karatun yara.

APC ta kara kudin asibitoci.

APC ta kara kudin makaranta.

APC ta kawo durkushewar gattalin arzikin jihar.

Da dai sauran dalilai dasuka kawo.

0 comments on “Anraba Takardun Gargadi Akan Kar a Sake Zaben Jam’iyar APC a Kaduna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *