Kannywood

GIDAN BADAMASI SEASON 4 EPISODE 2 – HAUSANOVELS.ORG.

Zamu gabatar muku da shirin nan mai dogon zango na kamfanin kannywood da ake gabatarwa da hausa mai suna gidan Badamasi season 4 episode 2 wanda ake haskawa a tashar arewa 24.

MENENE GIDAN BADAMASI season 4?

Gidan Badamasi wani shirine da ake gabatarwa da yaren hausa mai dogon zango na barkwanci a masana’antar kannywood wanda ake ta dauki ba dadi tsakanin wasu makwadaita kuma jara babbun yaya da kuma wani marowacin uba,Alhaji Badamasi.

Alhaji Badamasi dattijo ne mai kimanin shekaru 70 da doriya, yayi aure da dama a rayuwarsa, inda ya haifi yaya masu yawan gaske, har takai cewa wadansu bai ma san dasu ba.A shirin wasan kwaikwayon anfara kai ruwa rana ne a lokacin da alhaji badamasi yayiwa yayan nasa alkawarin kudi kimanin naira miliyan 5 ga kowane mutum daya, amma yakasa cikawa.

Daga nan ne yaki ya kaure tsakanin marowacin uban dakuma hada mammun yayan.Tashar Arewa24 ta bayyana cewa ba’a taba fim a kasar hausa irin gidan badamasi ba,

Shirin Gidan Badamasi hausa daga kannywood.

Shirin gidan badamasi shiri ne mai dogon zango, wanda tashar arewa 24 take haskawa a duk ranar juma’a da misalin karfe 8-9 na dare. Kamar yanda daraktan shirya fim din yafada, falalu a dorayi, ya bayyana cewa, GIDAN BADAMASI SEASON 4 EPISODE 2 shirine wanda aka kirkira domin bawa mutane nishadi da kuma sakasu farinciki.

“Shirin gidan Badamasi season 4 mun shiryasa ne domin saka mutane nishadi da farinciki”.inji falalu a dorayi.

KARANTA : Kannywood : Jaruman kannywood 10 wadanda asalinsu ba hausawa bane.

Zaku iya kallon shirin gidan badamasi a tashar a YouTube channel mai suna DORAYI FILM PRODUCTION ko kuma tashar AREWA 24 ko kuma ku dakko app dinsu dake Google play store mai suna AREWA 24 ON DEMAND domin kallon shirin.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button