Tuesday, 26 October, 2021

Ads Banner

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Joe Biden murna


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Joe Biden murnar lashe zabe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Joe Biden murnar lashe zabe
hausanovels.org

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Sabon Shugaban kasar Amerika watau joe bedan murnar lashe zabe.

A wata sanarwa da shugaban kasar Nigeria ya fitar a shafinsa na sada zumunta da instagram.

Ya nuna farin cikinsa da kuma taya murna ga sabon zababben shugaban kasar amurika.

inda ya ke cewa, Hakika joe bedan sai a tayaka murna da ka samu nasarar lashe zaben a cikin wannan mawuyacin halin da duniya ke ciki.

Wannan kuma ba karamar nasara da ci gaba ba ne ga tafiyar damocaradiyya ta duniya ba.

ya kara da cewa tabbas demokoradiyya ita ce salon mulki da ya fi cancanta duniya ta dore da shi.

ba dan komai ba kuwa, sai dan kasancewar ta tsari da ke bawa kowane mahaluki damar ya zabi wanda ya dace ya zame masa shugaba.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

ya ce demokoradiyya ita ce hanya mafi sauki ga dukkan al’umma da za su bi domin dora ko sauke shugabanninsu cikin lumana ba tare da tada kura ba.

Haka kuma talakawa su ne rukuni mafi karfi a tsarin demokoradiyya ba yan siyasa ba, domin kuwa su ne ke da karfin jefa kuriunsu a mazabu daban-daban na cikin kasa domin su kai yan siyasa ga karagar mulki.

Dimokoradiyya na martaba ra’ayim mutane ta yadda ta ke basu damar juya salon mulki daga kabila zuwa kabila ko daga yanki zuwa yanki cikin lumana.

 

Munsan zababben shugaban kasar amurika na da kyakkyawan tarihi. wanda da shi ne muke fatan ya kawo cigaba da kuma canci ga al’ummar duniya baki daya.

Daga karshe ina kira ga shugaba joe bedan da ya yi amfani da salonsa na kwarewa wajen tunkarar kalubalen da ke tattare da rikicin siyasa ta duniya domin hada kan kasashen duniya baki daya.

Sannan kuma ina fatan zai samar da kyakkyawar alaka tsakanin nahiyarsu da kuma nahiyar Afrika cikin mutunta juna da girmamawa.

Karanta Munirat Abdussalam ta fitar da sanarwar fita daga musulunci

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

One comment on “Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Joe Biden murna

[…] Karanta¬†Sakon Muhammadu Buhari zuwa sabon shugaban America […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *