Friday, 24 September, 2021

Ads Banner

An farmaki ibrahim maishunku hari a hanyar abuja


An farmaki ibrahim maishunku

An farmaki ibrahim maishunku

An farmaki ibrahim maishunku

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana yadda wani lamari ya auku ga fitaccen jarumin kannywood watau ibrahim maishunku da abokansa hari a hanyarsu ta dawowa daga abuja.

Rahoton ya bayyana yadda yan bindigar su ka farmaki wadannan bayin Allan maishunku ne shi da abokan tafiyarsa a kan hanyarnan da ke tsakanin abuja zuwa kaduna.

Rahoton ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane ne su ka tarye hanyar inda suka bude wuta ga fasinjojin, wanda aka kwashe akalla mintuna talatin ba kakkautawa.

Haka kuma a yayin bude wutar, akalla mutum talatin ne su ka jikkata sannan kuma mutum goma sun zama shekakku.

Har wa yau, sakamakon harin ya janyo har masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da aboki kuma dan uwa ga ibrahim maishunku.

Ibrahim maishunku ya ce abu ne da ya zama dole su bayyana wa duniya halin da ake ciki domin a sanya wanda aka yi garkuwa da shi.

An farmaki ibrahim maishunku

Lamarin garkuwa da mutane ya zama ruwan dare mai gama duniya, musamman a yankuna da su ka hada da kaduna, da katsina, da zamfara, da kebbi, da wasu sauran jihohin da ke da makwaftaka da su.

Lamarin ya yi kamari sosai musamman a wannan lokacin da harkar tsaro ta tabarbare a nigeria musamman ma a yankin arewa da abun ta fi kamari.

Karanta Sakon Muhammadu Buhari zuwa sabon shugaban America

A yanzu haka dai bayan An farmaki ibrahim maishunku da abokansa da kuma yin awon gaba da abokinsu sai dai har yanzu ba wani karin bayani da aka samu dangane da batan nasa.

Muna fatan Allah ya bayyana shi cikin koshin lafiya.

A wani labarin kuma za ku ji cewa yamu baba mai wakar sambisa shi da zainab sambisa su na nan su na shirya wasu sabbin kayatattun wakoki cikin bidiyo a garin jos domin su nishadantar tare da farantawa masu bibiyar wakokin su.

sakamakon haka ne ma ya shirya wakokinsa sabbi irin su mai mata hudu, da marka mai tuwo, da wasu ma dadadan wakokinsa masu dauke da darasi a cikin su kamar yadda aka saba ji daga bakinsa a duk lokacin da ya fitar da sabuwar wakar sa.

Idan ba za a manta ba, mawakin a kwanakin da su ka shude ya yi tashen nishadantar da masoyansa da wakoki masu dadin gaske inda a kalla ya saki wakokin sun kai kimanin 6 shida, dukka kuwa a cikin wakokin nasa babu jagajan tagajan. Domin kuwa wakoki ne da su ka amsa sunan su wanda dukmai sauraro idan ya ji labarin hakika sai ya yaba masa.

Hakikanin gaskiya yamu baba da shi da zainab wadda a ke wa lakabi da sambisa ma’ana Zainab sambisa sun yi kokari sosai a cikin wakar sambisa tun daga ta farko har izuwa na baya bayannan wanda su ka hada da kai ka zagi matar sarki da anan na yada kudi na da sauransu.

Yamu baba shi da zainab sambisa sun kasance masu neman aiki ne a cikin duk wata hanya da ta dace domin ganin sun faranta ran masu kallonsu, mabiyan su da kuma dukkan masoyansu baki daya.

An farmaki ibrahim maishunku

Ita ma zainab sambisa duk da kasancewarta sabon shiga a masana’antar kannywood, amma hakan bai hana shi fuskantar kalu bale ba.

Sannan ita ma zainab sambisa din a cikin lokacin ne a ke samun zakakurai su fito daga cikin ragwagi.

0 comments on “An farmaki ibrahim maishunku hari a hanyar abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *