Saturday, 25 September, 2021

Ads Banner

Ba a kawomin sammaci ba inji rahama sadau


ba a kawo min sammaci daga kotu ko yan sanda ba inji rahama sadau

Ba a kawomin sammaci daga kotu ko yan sanda ba

Ba a kawomin sammaci ba inji rahama sadau

Fitacciyar jarumar kannywood Rahama sadau, ta ce Yan sanda ko kotu basu kawo mata sammaci ba inji rahama sadau.

jarumar ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na twitter, inda ta ce:

mutane da dama suna turo min sakwanni yau akan cewa wai yan sanda sun kama ni bayan kuwa ni bani da wata masaniya akan wannan batun.

Asali ma ni ban san inda wannan labarin kanzon kuregen ya fito ba.

dan haka ina kira ga mutane da su daina yada labari da bay da tushe bare makama.

Nikam ba wanda ya kawo min sammace daga kotu ko wurin yan sanda. Haka zakalika ba wanda ya kamani.

Ba a kawomin sammaci ba inji rama sadau

Haka dai Rama Sadau ta dinga jero posting kala daban-daban domin ta tabbatarwa da duniya cewa ita ba wani wanda ya kawo mata sammace ko ya zo kamata, kawai dai batu ne da mutane su ka saba yi a social media.

Ba a kawomin sammaci ba inji rama sadau

Inda da zara dan karamin abu ya fara to sai kaga ana ta yayata shi, ana kuma sanya kage da karin gishiri a cikinsa wanda hakan ba adalci ba ne.

Hakika Rahama sadau ta kasan ce fitacciyar jaruma a kannywood, sai dai duk da ficen da ta yi , hakan bai hanata yin wasu abubuwa na rashin da’a wanda su ka saba ka’idar addininta da na masana’antarsu ta kannywood.

Ba a kawomin sammaci ba inji rama sadau

Wannan abun ba karamin hatsaniya da cacar baki ya ke janyowa kannywood ba a cikin alummar Hausawa.

karanta Rahama Sadau na cin karenta ba babbaka a kannywood 

Bugu da kari rahama sadau ta yi kira ga bloggers da su daina wallafa labaran karya da basu inganta a kanta ba, wanda ta ce ya kamata a barta ta hutawa ranta.

Kamar dai yadda aka sani a aladar yan arewa da ma sauran sassan duniya baki daya, aduk lokacin da mutum ya zama tauraro, kokuma in ce ya zama wanda dunuya ke kallo ko sauraro to dole ya kasance mai taka tsantsan da abunda zai yi ko zai fada.

Su kuma bloggers ko kuma na ce yan jarida da yan social media yana daga dabiarsu ya kasance da mutum ya yi wani abu dan kadan, musamman ma ida ya kasance tauraro to sai sun dauki wannan abun su dinga yayata shi.

a saboda haka ne ma rahama sadau ya ke kira a garesu da su yi mata adalci aduk wani abu da za su wallafa wanda ya shafi rayuwarta.

2 comments on “Ba a kawomin sammaci ba inji rahama sadau

[…] karanta ba-a-kawomin-sammaci-ba-inji-rahama-sadau […]

[…] karanta Ba a kawomin sammaci ba inji Rahama Sadau […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *