Friday, 24 September, 2021

Ads Banner

Munirat Abdussalam ta fita daga addinin Musulunci


Hausanovels.org
Munirat Abdussalam ta fita daga addinin Musulunci
Hausanovels.org

Munirat Abdussalam ta fita daga addinin Musulunci.

Innalillahi wa inna ilaihi rajiuun Munirat Abdussalam ta. Fitacciyar mai tallar magungunan gyaran zaman aure na bangaren mata da maza wadda ta yi fice a kafar tura video ta yanar gizo watau youtube da kuma kafar sada zumunta na instagram wadda aka fi sani da Munirat Abdussalam ta fitar da sanarwar cewa ta fita daga addinn musulunci gabaki daya.

Munirat Abdussalam ta wallafa wani rubutu ne a shafinta na  sada zumunta na instagram inda ta yi ikirarin cewa, Daga rana irin ta yau kar wanda ya kara jinginata da addinin Musulunci.

matar ta ce, tun da ya amshi kalmar shahada a cikin shekaru biyu da suka shude, bata samu wata karuwa ko cigaba ba face tsangwama da barazanar shika, da kuma zaginta da ake yi.

Baya ga wannan ma ta kara da cewa an saka sunanta a gaba duk abinda ta yi wanda ta ke gani daidai ne a rayuwarta ko da ya saba dokar addinin muusulunci to musulmai basa yin shuru da bakinsu, sai su kama ambatonta suna fadar albarkatun bakunansu wanda ya ke kuma daidai da tsarin Allah, amma sun manta da cewa ra’ayinta ne ta bi ba wai dokar Allah ba.

Kwata-kwata musulmi  basa nunamin wata kauna ko ko su jawoni a jikinsu a matsayina na yarinya mai raye cikin maraici bayan kuma sun san cewa ni marainiya ce wadda ta ke rayuwa cikin wannan matsin rayuwa ita kadai.

Ba abinda na fi so wurin musulmai face ja a jiki da kuma shakuwa, wanda hakan bai samu ba. saboda haka gaskiya ni na gaji kawai, don haka ne ma na yanke hukuncin yin ridda na bar addinin musuluncin gabaki daya.

Nidai abinda na yarda da shi a raina shi ne, imani na yana ga mahaliccina, wannan kenan.

A yanzu ya ku musulmai ku yi sani cewa inhar kuna so ku shekeni to lallai ku aikata hakan amma ni na riga na yi abinda na yi niyya kuma ba gudu ba ja da baya.

Munirat Abdussalam ta fita daga addini Musulunci
hausanovels.org

karanta Aika-aikar da Rahama Sadau ke aikatawa a Kannywood

Kamar yadda ku ka ga bayanin da ya gabata wanda a cikinsa mu ka yi tambihin abinda Munirat Abdussalam ta wallafa a shafinta na instagram wanda ya shafi

Munirat Abdussalam ta fita daga addinin Musulunci.

kuma kamar yadda ku ka gani daga hoton da ke sama domin ku tabbatar tunda kuwa Hausawa na cewa gani ya kori ji, haka kuma waka a bakin mai ita ta fi dadi.

Masu karatu in ba ku manta ba Munirat Abdussalam dai daman ba yaune ta fara yin irin wannan abun ba. saboda idan aka bibiyi tarihi za mu ga cewa ta sha shiga ta fita daga wannan addini zuwa wancan, wanda nazari ya nuna cewa bata dauki canza addini a bakin komai ba. Daman dai ba wani abu ta sani a cikin addin musuluncin ba kawai dai sunan tana musulma ce kawai.

Amma za ku ga cewa addinin bai hanata aikata duk wani abu da ta ke da ra’ayin aikatawa ba. Saboda haka kuma sanin kowa ce cewa shi addinin musulunci ba addinin jeka na yika ba ne ba, a’a addini mai dauke da tsari mai kyau da kuma dokoki wanda ko ba a fada maka ba indai ka kalli mai kiyaye wadannan dokokin addinin za ka iya banbanceshi da wanda bai damu da su ba.

Saboda haka a kaidar musulunci dan mutum ya yi ridda aka mishi wa’azi aka bashi lokaci bai dawo ba to hukuncinsa shika ne amma ita Munirat Abdussalam ta bar addini Musulunci kuma zata amshi hukuncin ta idan ta koma ga mahalicci.

Duk da cewa kai a matsayinka na musulmin kwarai baka da wani mataki na hukunci da zaka iya dauka a kan ta ba, amma zai fi kyau ka kyamaci abinda ta yi a cikin zuciyarka sannan ka nisanci duk wani abu nata da ka sani tun daga youtube channel har following dinta a social media.

Muna fatan Allah ya shiryar da ita ya nuna mata gaskiya, ya kuma ceto ta daga fadawa cikin kogin duhu, amin.

Sannan muna kira ga dukkan wani mai imani da ya kyautata alakarsa da mahaliccinsa da kuma sauran al’umma domin duniya ba gidan zama ba ce.

Innalillahi wa inna ialaihi rajiuun’

Munirat Abdussalam ta fita daga addinin Musulunci.

 

One comment on “Munirat Abdussalam ta fita daga addinin Musulunci

[…] Karanta Munirat Abdussalam ta fitar da sanarwar fita daga musulunci […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *