Friday, 03 December, 2021

Manyan Kungiyoyi Sunfara Magana Akan Bacewar Dadiyata.


Abubakar adiya
Abubakar dadiyata tareda dan takarar gwamnan jihar kano abba k yusuf

A ranar 30 gawatan August na kowace shekara ake tunawa da mutanen da aka nema aka rasa ta a dalilin daukesu, tauye musu hakki ko kuma tsaresu.

Wata kungiya ta access to Justice (a2justice) tayi kira da gwamnati tarayya ta binciki lamarin bacewar abubakar idris,wanda akafi sani da DADIYATA.

Kungiyar a2justice tayi magana ne yayin da ake bikin tuna mutanen da aka nema aka rasa a duk kasashen duniya.

Kungiyar tace bacewar Dadiyata yajefa Danginsa dakuma masoyansa cikin zullumi rudani da kuma dar-dar.

A ranar 2 gawatan agustan shekarar 2019 ne dai wasu mutane da ba’asan kosu wanene ba suka dauke wannan malamin har yau kuma babu labarinshi.

0 comments on “Manyan Kungiyoyi Sunfara Magana Akan Bacewar Dadiyata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *