Friday, 03 December, 2021

Wani magidanci ya kashe matarsa saboda tace baya gamsar da ita.


Ana tuhumar wani magidanci mai suna, Stephen nyageri mauti, da laifin kisan matarsa faith nyatichi saboda tace masa bata gamsuwa dashi a wurin aure.

Lamarin wanda ya faru a yankin dake nairabi a kasar kenya ranar 3 gawatan October 2021.

A rahoton da jaridar LIB ta ruwaito ya bayyana cewa, rahoton da aka karanto a kotu ranar 14 ga watan oktoba ya bayyana cewa, Marigayiyar ta ziyarci unguwar kangemi hill inda suka kama hayar gida bayan ta baro nyeri inda suke zaune a matsayin mata da miji.

Jaridar legit.nghausa ta ruwaito cewa marigayiyar tabar gidan mijint ta shaida masa zataje ziyarar wata ‘yar uwarta, bayan wani lokaci daya gabata dawo ba sai ya kirata sai tace tatafi kauye.

Sai dai wanda ake zargi ya tambayi yayan matar tasa ko suna da yan uwa a inda marigayiyar tace zata? Inda mutumin yace basu da yan’uwa acan.

A ranar 1 gawatan matar takira mijnta a waya tace zata kai masa ziyara tunda bashi da lafiya da lafiya kamar yanda rahoton ya bayyana.

Bayan takaimasa ziyarar ne ta dafa abincin rana sukaci tare sannan suka fita tattaki,sannan suka dawo gida, bayansun dawo matar ta dafa abincin dare sukaci sannan suka kwanta.

A cewar rahoton da yan sanda suka fitar, sun tattauna tsakaninsu amma basu cimma matsaya saboda matar kuka ta dingayi ahaka sukayi kwanciyar aure.

A ranar 3 gawatan October bayan sun tashi daga barci sai matar ta dafa shayi, suna cikin karyawa sai mutumin yacigaba da lallabarta akan kada ta rabu dashi ta auri wani.

A wani jawabi da yakeyiwa yan sanda, wanda ake zargi ya nemi yafada mata gaskiya kan zargin cewa tana zaman dadiro da wani mutumin a waje,yace daga nan matar tafara masa ihu tana cewa shi ba cikakken namiji bane a wurin kwanciyar aure.

Wanda ake zargi ya damketa ya rufe mata baki nemi ta daina masa ihu.

Bayan tayi shiru yayi tsammanin ta hakura ne, amma sai ya lura ta suma, ya kira makobta suka garzaya da ita asibiti, inda acan aka tabbatar musu ta rasu.

Babban majistare na nairabo ya bada umarnin ayiwa wanda ake zargi gwajin kwakwalwa kafin ayanke masa hukunci ranar 17 gawatan october 2021.

0 comments on “Wani magidanci ya kashe matarsa saboda tace baya gamsar da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *