Labaran Duniya

Zan kashe kaina idan har ba’a raba aurena da matata ba-inji wani magidanci.

Wani magidanci mazaunin jahar ibadan mai suna,amos akinkolu, yanemi kotu data raba aurensa da matarsa funmilayo, bayan dasuka kwashe sama da shekaru 30 a tare.

Magidancin ya bayyanawa kotu cewa yana bukatar araba auren saboda ya gano matar tasa fasikace.

“Nagaji da auren funmilayo saboda nagano cewa tana mu’amala da maza a waje, nagaji da aurenta saboda bin mazan datakeyi barazana ce ga rayuwata” inji shi kamar yanda mujallar RIGAR YANCI INTERNATIONAL ta wallafa.

“Idan har kotu bata raba aure naba to zan kashe kaina saboda ina tunanin hakane kwanciyar hankali na”.

Sai dai kuma a nata bangaren matar tasa ta bayyana cewa karyane kawai yakeyi mata,tace tunda sukayi aure mijinnata bai taba kamata tana lalata da wani ba.

Daga karshe kotu ta raba auren bayan yayan ma’auratan 5 dasuka haifa sunsa baki akan kotu ta raba kowa ya huta.

Alkalin kotun, mrs imoleayo akinrodoye tace yaya uku cikin guda biyar da ma’auratan suka haifa zasu tafi gurin mahaifiyarsu saboda karancin shekaru.

Sannan tace mijin zai bawa matar dubu naira 30000 wanda zata biya kudin hayar gidan da zata zauna ita da yayanta,sannan ya biya kudi naira 10000 kudin kwasar kayanta daga gidansa.

Bayan haka kuma zai rika aika mata da naira 30000 duk wata kudin ciyar da yayansu uku wadanda take tare dasu.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button