KannywoodUncategorized

ko ni an nemi yin lalata da ni dan a sakani a film a kannywood

ko ni an nemi yin lalata da ni dan a sakani a film a kannywood

Wata mata da ba’a tabbatar wacece ita a cikin matan kannywood ta fito ta bayyana cewa batun neman mata da lalata kafin a saka su a film gaskiya ne, kuma wannan ne ma dalilin da ya sa bata yi suna ba a kannywood.

Matar dai da ba a ambaci sunanta ba ta fito a cikin wani bidiyo inda ta ke jaddada batun naziru sarkin waka da ya yi na cewa ana yin lalata da mata kawai dan a sakasu a film a cikin masana’antar ta kannywood. Matar ta c wannan batun fa ya kamata duniya ta daina kokanto a kansa domin kuwa ko ita a karan kanta lokacin da ta shigo industry sai da aka dinga nemanta da lalata tana kiyawa, a sakamakon haka ne yasa bata samu ta yi suna a masana’antar ba.

Matar ta ci gaba da cewa, duk wani abun azo a gani da ta samu a kannywood ba a sanadin film ba ne sai dai a sanadin waka. Inda ta bayyana nasarorin da ta ci a wannan masana’anta kama daga samun kyautuka hak kuma zuwansu gidan shugaban kasa duk a dalilin waka ne ba film ba.

Sai dai kuma kasancewar a dandalin tiktok da instagram ne ya saki wannan bidiyon, sai ya kasance kwatakwata masu comment wato tofa albarkacin baki basu goti bayan ikirarin da ta ke yi ba. Inda wasu ma su ke cewa ta yi hakan ne domin yin maula ga naziru sarkin waka ganin yadda ya gwangwaje ladin chima da fati slow da ruwan nerori.

Tun dai daga lokacin da naziru sarkin waka ya furta cewa ana lalata da mata kafin saka su a kannywood, sai kuma dukkan wata wutar rikici da kalaman ladin chima su ka jawo su ka karkata zuwa sabon rikicin da yasa hatta wadanda basu kai su ka kawo ba ma na fitowa su yi surutansu da sunan yan kannywood wanda ake ganin hakan a matsayin zubewar mutuncin masan’antar.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button