Uncategorized

YANZU-YANZU: Nafisa Abdullahi Ta bayyana ficewarta daga cikin Shirin Labarina Sannan kuma ta bayyana dalilinta.

YANZU-YANZU: Nafisa Abdullahi Ta bayyana ficewarta daga cikin Shirin Labarina Sannan kuma ta bayyana dalilinta.

fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Nafisat Abdullahi,wacce akeyiwa lakabi da Sumayya acikin shirin labarina mai dogon zango wanda kamfanin saira movies suke kawo wa ta bayyana ficewarta daga cikin shirin gaba-daya.

Jarumar Ta sanar da Hakan acikin Shafinta na dandalin sada zumuntar Facebook,a Daren asabar 1 ga sabuwar shekarar 2022,inda ta bayyana ficewar tata kan karancin lokaci saboda karatu datakeyi, sannan kuma ga wani sabon shirin kamfaninta datake shirin fara dauka.

Dama masu kallo sun dade suna ganin take-taken daraktan fim din, aminu saira, kan fitar da jarumar daga cikin shirin tun kafin ta bayyana ficewartata a yau bisa la’akari da yanda yanuna anyi garkuwa da ita sannan kuma yanuna cewa bom ya tashi da fuskarta a wannan makon.

Sai dai kuma wasu masu hasashe naganin cewar kamar rashin jarumar (nafisa abdullahi) zai iya kawo koma baya ko kuma tangarda duba da yanda jarumar ta kware da aktin akan rol din da akabata a fim din

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button