Friday, 24 September, 2021

Ads Banner

Takashe mijinta bayan anyimata auren dole a


Wannan matar da kuke gani itace takashe mijinta bayan anyimata auren dole.

Sunanta Rumasa’u Muhammad shekarunta 19, tana zaune a jihar adamawa garin wuro yanka a karamar hukumar shelleng.

Andaura mata aurene da wani mutum wanda bashi takeso ba mai suna muhammad adamu dan shekara 35,tanemi mijin nata yasaketa amma yaki, tabi duk hanyar dataga zata samu yasake ta amma yabujire yaki sakinta, daga karshe dai shine ta kashe shi tahanyar burma masa wuka yana barci.

Kafin akai mutumin asibiti bayan ta buga masa wuka rai yayi halinsa (ya mutu)yan sandan shelleng sun kama matar.

Bayan yansanda sunyi bincike sai suka gano cewa sati uku dasuka gabata akayiwa matar aure tareda marigayin mijin nata wanda takashe, anyi auren a ranar 6-8-2021.

Kwamishinan yan sandan jihar adamawa,CP ALIYU ADAMU ALAJI yabada umarni akan agudanar da bincike akan kisan, kuma yabawa iyaye shawara akan suguji yiwa iyayensu auren dole.

0 comments on “Takashe mijinta bayan anyimata auren dole a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *