Tuesday, 26 October, 2021

Ads Banner

Jaruma Rahama Sadau da tabargazarta a kannywood


rahama sadau

Jaruma Rahama Sadaurahama sadau

Fitacciyar yar wasan hausa a kannywood mai suna Jaruma Rahama Sadau ta kasance jaruma mafi tarin mabiya a masana’antar kannywood, wanda hakan ya janyo ta samu followers fiye da kowa a shafukanta na sada zumunta.

Duk da irin yadda ta tara mabiya, hakan bai hanata aikata katobara da aika aika ba.

Domin kuwa tun shekaru da dama da suka shude Jaruma Rahama Sadauu ke aikata wasu abubuwa da suka tsarin da kuma dokar addininta na musulunci.

A cikinb irin abubuwan da ta ke aikatawa za mu ga abubuwa kamar haka:

dafarko dai Jaruma Rahama Sadau ta taba fitowa ta kira yan arewa kauyawa kuma ta cea barta ta girbi abinda ta shuka a daina yi mata nasiha.

Abinda ya janyo hakan kuwa ba wani abu ba ne face wani hotuna da ta dauka tare da wani mawaki da ake kira timaya. Wanda a cikin hotunan an ga Jaruma Rahama Sadau na rumgumemeniya da mawakin.

wannan ba karamin cece ku ce ya janyo mata b

Idan za mu yi duba da yadda rayuwar Jaruma Rahama Sadau ta gudana a baya za mu iya tuna cewa ta taba tafka wata kasassabar da ta sanya wani mashahurin malamin sunna kuma shugaban hisbah na kano na wancan lokacin ya yi wa,azi mai dauke da nasiha a kanta, amma a bisa mamakin sai ga shi ta sambada masa zazzafan raddi.

A yanzu kuwa Rahama Sadau ta sake sakin wasu hotuna da ke nuna gadon bayanta da wasu sassan jikinta, wanda hakan ya janyo aka dinga yi mata martani masu zafi kala-kala. wanda  yanzu haka har an samu wani wanda ya yi amfani da abinda ta yi ya yi batanci ga fiyayyen halitta (SAW).hausanovels.org

karanta Allah ne sheda complete hausa novel

Wannan lamari da Rahama Sadau ta janyo ya fusata a-lummar musulmi wan da ya sa aka dinga la’antarta.

Bugu da kari abokan huldar  Rahama Sadau na masana’antar kannywood su ka fito su na yi wa Jaruma Rahama Sadau tofin Alatsine.

Daga karshe dai Rahama Sadau ta fito cikin shiga ta kamala inda ta ke neman afuwar Dukkan duniya tare da nuna nadamar ta a fili wanda ya kai ta ga zubar da hawaye.

Allah ya kara daukaaka musulunci da musulmai baki daya.

duk da cewa rahama sadau ta zama wankakkiya da mai a masanaantar kannywood domin kuwa idan za a kwatanta irin yadda ta ce tafka ta’asarta a masana’anta amma hukumar tace finafinai kawatau moppan ta kasa daukar mataki a kanta, lallai abun ba karamar alamar tambaya ce ke tattare da shi ba.

saboda idan ba za mu manta ba a baya akwai jarumai da dama da su ka aikata laifuka da ko rabin nata basu yi ba amma sai da aka dauki matakai masu tsauri a kansu irin cinsu tara da basu suspension ma’ana dakatarwa ta wani dan lokaci dko kuma korarsu ma baki daya daga kannywood.

jarumai irin su Adam A zango, da Naziru sarkin waka da tijjani asasi da garzali miko da sauran su bwadanda aka  yiwa tsattsauran hukuncin da ya kai ga kora wasu har da dauri a gidan yari amma duk da haka ita rahama sadau abinta duk da ya kai ga janyo batanci ga Rasulullahi(SAW) amma gashi an kasa daukar matakin komai a kanta.

2 comments on “Jaruma Rahama Sadau da tabargazarta a kannywood

[…] karanta Aika-aikar da Rahama Sadau ke aikatawa a Kannywood […]

[…] karanta Rahama Sadau na cin karenta ba babbaka a kannywood  […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *