Labaran Duniya

ABUN TAKAICI : Da ya kashe mahaifinsa akan gona.

Wani mutum mai suna haruna buba dan shekaru 32, ya kashe mahaifinsa akan gona a jihar gombe.

Matashin ya aikata kisan biyo bayan wani sabani daya hadashi da yayansa,yayin dashi matashin yake zargin babansa ya bawa yayan nasa babbar gona.

Bayanai sun bayyana cewa, mahaifinnasu, Habu kuppe, yazone domin yin sulhu a tsakanin yan’uwan biyu,a lokacinne haruna ya yanke shi a kai da da baya da adda, inda anan takeutumin yace ga garinku nan.

A wani rahoto da jaridar Daily trust ta fitar ya bayyana cewa, bayan da haruna ya aikata wannan danyen aiki, sai yatafi wurin kallo a kauyen, inda acan yan sanda suka kamashi.

Kakakin yan sandan jihar,mallum buba yatabbatar da faruwar al’amarin,yace da zarar angama bincike za’a mika mai laifin kotu.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button