Friday, 03 December, 2021

Barayin waya a kano sun hallaka wani matashi mai shekaru 30 a kano.


Wasu masu kwacen waya akan Adaidaita sahu sun hallaka wani matashi dan karamar hukumar fagge a kano.

Matashin mai suna abdullahi bala dan kimanin shekaru 30, ya hadu da ajalinsa a ranar juma’a bayan yataso daga aiki yana shirin zuwa ta’aziyya tsakanin titin zungeru road zuwa festing road.

KARANTA : SUBHANALLAHI WANI MATASHI YA RATAYE KANSA A KANO

Wani dan’uwan marigayin mai suna,Abdul-aziz bala, ya shaidawa jaridar DAILY TRUST cewa an sokawa marigayin bala wuka ne da misalin karfe 6:45 na yammacin juma’a.

“Ya hau adaidaita sahune akan hanyarsa ta zuwa ta’aziyya birgade, baisan cewa mutanen ciki ba masu adaidaita sahu bane barayin wayane ba”.

“Suna cikin tafiya sai suka nemi yabasu wayarshi, shikuma sai ya wurgata waje domin neman taimakon jama’a kan abunda yake faruwa, ganin haka sukuma barayin sai suka caka masa wuka a cinya sannan suka gudu.

KARANTA: ABUN TAKAICI : DA YAKASHE MAHAIFINSA AKAN GONA

“Ankira yansanda, inda sukayi hanzarin fara kamen masu adaidaita sahu,sai dai kuma har yanzu ba’aga wadanda sukayi aikata aika-aikarba”.

Yacigaba da bayyana cewa “yan sanda ne suka kaishi asibitin murtala Muhammed, mu yan’uwansa sai ranar asabar sannan aka sanar damu mutuwarsa”.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar kano, DSP Abdullahi haruna kiuawa ya tabbatar da faruwar al’amarin, sanna yace yanzu haka ancafke mutane biyu da ake zargin sunada alaka da kisan kan, kum nan bada jimawa ba za’a gurfanar dasu a gaban kotu.

Sannan yace ana cigaba da bincike domin kamo sauran wadanda aka aikata ta’asar dasu.

2 comments on “Barayin waya a kano sun hallaka wani matashi mai shekaru 30 a kano.

[…] KARANTA : Barayin waya a kano sun hallaka wani matashi mai shekaru 30 a kano. […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *