Labaran Duniya

Ya kashe kanwarsa har lahira saboda tana da samari 6 a WhatsApp.

Wani abun takaici kuma abun allah wadai yafaru akasar Zimbabwe, inda aka gabatar da wani matashi bisa kamashi da zargin kashe kanwarsa.

Alkalin babbar kotun bulawayo dake kasar Zimbabwe, justice maxwell takuva, ya yankewa saurayin da aka kama da zargin kashe kanwarsa hukuncin shekaru 8 a gidan gyaran hali.

Matashin mai shekaru 27 yayiwa kanwarsa mai shekaru 16 duka wanda yayi sanadin mutuwarta bisa zarginta da rashin kamun kai.

Saurayin mai suna, Terrence Tarisai na clifton park ya musanta zargin da ake masa na kashe kanwarsa mai suna Trhypine, Ta hanyar duka bayan ya bincika wayarta yashiga dandalin sada zumunta na WhatsApp yaga ta tara samari 6.

Jaridar LIB Ta ruwaito cewa, tarisai yadawo gida ranar 22 gawatan yuli 2020 amma bai tarar da Trhypine ba sai dai kanwarta yar shekara 10 ita kadai a gida kamar yanda rahotanni suka bayyana.

Trhypine yar makaranta ce ajinta 3 a ascot high school dake gwaru,ta dawo gida karfe shida na yamma, inda ta bayyanawa yayannata cewa a shago ta tsaya.

Duk da bayanin datayi amma yayannata bai yardaba, inda ya amshi wayarta yaduba, sai yagano cewa tanada samari 6, daga nan yazarge ta da rashin kamun kai.

Ganin hakanne yasa trhypine guduwa gidan antinta, washe gari da safe antinta ta rakata gida.

Duk da haka sai da yazaneta, kuma ya bukaci ta tsaida alakarta da wadancan samarin.

Bayan haka kuma sai yaci gaba da dukanta, sai da tafara korafin cewa tanajin sanyi sannan antinta ta dora ta akan gado don ta huta, wanda sanadiyyar hakanne tarasu bayan kwashe wasu yan sa’o’i tana bacci.

Bayan angano tarasune yan sanda suka kama matashin suka tafi dashi.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button