Labaran Duniya

Wani Uba ya cire nonon yarsa yar shekara 8

Rundunar yansandan jihar legas sunkama wani uba wanda ake zargi da cirewa yarsa nono ta hanyar amfanida dutsen guga mai zafi.

Bayanai sun nuna cewa,mahaifin yarinyar ya aikata mata hakane sakamakon ganinta tafara ‘kirgan dangi’ ma’ana tafara balaga.

A yanzu yarinyar Tana asibiti cikin mawuyacin hali ana kula da ita sakamakon ta’asar da mahaifinta mai suna mista Banjo ya aikata mata.

Wata kungiyar kare hakkin yara da marasa galihu ce takai karar mahaifin yarinyar gaban yansanda,kuma kakakin yansandan jihar legas, DSP asijobetu bai musanta labarinba inda yace zasu gudanar da bincike,kamar ynada rahoton BBC HAUSA ya tabbatar.

Rahotanni sun bayyana cewa tuni jami’an hukumar yansandan jihar suka kama da iyayen yarinyar.

Shugaban kungiyar kare hakkin yara marasa galihu,kwamred Ebenezer omajalile ne yakai karar, ya shaidawa BBC HAUSA cewa mahaifin yarinyar mista Banjo wanda ake kira panel”ya gurje tareda kone nonon yar tasa”

Yace” mahaifin yarinyar yayi amfani da dutse mai zafi yalullube da tsumma har saida ya tabbatar dacewa ya illata nonon yarinyar”

Mahaifiyar yarinyar tace a kullum mista banjo sai ya daki yarinyar tasa mai suna Aisha, sai sai kwamared Ebenezer yace “a gaban mahaifiyar uban ya aikata wannan ta’asar”.

Daga karshe dai mahaifin yarinyar ya amsa cewa tabbas shiyayi wannan ta’asar inji kwamared Ebenezer.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button