Kannywood
Trending

DUNIYA TAZO KARSHE : Yadda Jarumar Kannywood ta rungume wani saurayi a bainar jama’a ba kunya.

Ana zargin wata daga cikin Jarumar kannywood da rungume wani saurayi a bainar jama’a ba kunya ba tsoron allah.

Wani hoto dayake yawo a dandalin sada zumunta na Facebook ya jawo cece-kuce, bayan da aka ga wata budurwa rungume da saurayi,wacce ake zargin budurwar jarumar kannywood ce.

A satin da muke ciki babu labarin daya yadu kamar wutar daji irin wannan labari na ganin wannan hoto, wanda ake zargin jaruman masana’antar shirya finafinan hausa na kannywood ne aciki.Inda jama’a da dama suke Allah wadai da abun indai ta tabbata Hakane.

Sai dai kuma a wani bincike da muka gudanar mungano cewa wannan labari ba gaskiya bane, domin kuwa wannan hoto bashi da alaka da duka jaruman kannywood mata da maza.Inda muka gano cewa shi kansa hoton bana jarumai bane, ma’ana, bana yan wasan kwaikwayo bane.

Duk dayake dai Har yanzu bamu gano asalin hoton ba, amma dai mungano cewa bashi da alaka da jaruman kannywood kwata-kwata, domin acikin Hoton babu jarumar data fitar da hoton a kafafen sada zumuntar ta.

Saboda haka muke rokon jama’a dan allah su kula su daina yada jita-jita.

KARANTA : YANZU-YANZU : MARYAM YAHAYA TA WARKE HAR TAFARA FIM A MASANA’ANTAR KANNYWOOD.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button