Tuesday, 26 October, 2021

Ads Banner

Jaruma momee gombe ta yi nasarar siyen sabuwar mota


momee gombe ta sayi mota

Jaruma momee gombe

Jaruma momee gombe. ta yi nasarar siyen motarta ta farko kuma sabuwa kirar peogeot bayan nasarorin da ta samu a kannywood a shekara 2020.

Tun lokacin da fitaccen mawakinnan Hamisu Breaker ya fara yin wakokinsa na video tare da momee gombe, sai ga shi jarumar ta fara samun amsuwa matuka a wurin mutanen da ke jin yaren Hausa a daukacin fadin duniya ga baki daya.

Sai dai duk da irin amsuwa da jarumar ta samu, ba a taba ganin amsuwa irin wadda ta samu a wakar da su ka yi da Hamisu Breaker Dorayi ta jarum ba.

Jaruma momee gombe

Hakika Jaruma momee gombe ta samu amsuwa sosai a wurin mutane a yayin da ta fito a matsayin tauraruwa a cikin wakar hamisu breaker jarumar mata.

Wanda tun daga wannan lokacin sai mafi yawan producers da directors da kuma mawaka su ka dinga sanya momee gombe a cikin dukkan hausa film dinsu da kuma wakokin hausa, hakan kuwa ya haifar wa da momee gombe farin jini da daukaka sosai.

Jim kadan bayan fara samun wannan daukaka sai ga shi kwatsam Jaruma momee gombe har ta fara mallakar abun hannunta, kamar yadda sauran jauram kannywood mata da su ka gabata irin su Maryam Yahay, da su Hadiza Gabon, da Nafisa Abdullahi, da Rahama Sadau, da Hafsat Idriss Barauniya da sauransu su ka mallaka.

A yanzu haka dai a cikin satin da ya gabata momee gombe ta yi nasarar siyen mota kirar 406.

Hakika jaruman kannywood da dama irin su Adam A zango da su Hamisu Breaker da wasu masu yawa sun dinga wallafa sakon tayata murna a shafukansu na dasa zumunta na instagram.

Mu ma muna taya jaruma momee gombe murnar mallakar mota, Allah ya tayata riko.

Jaruma momee gombe

karanta ba-a-kawomin-sammaci-ba-inji-rahama-sadau

Jaruma momee gombe ta kasance jarumar da ta fara fitowa a harkokin finafinai na kannywood amma daga baya ta yi auree, sai dai auren nata bai shude ba ko kuma ince bai dade ba ta

fito.

Sai dai kamar yadda tsegumi ya dinga yawo a kafafen yada labarai a wancan zamanin an rika rade-radin cewa Hamisu Breaker ne ya kashe auren momee gombe.

Wannan rade-radin da ya bazu a kafofin sada zumunta na zamani(social media) ya kasance jita-jita wadda bata tabbata ta fuskar shaidu da hujjoji ba.

A wani labarin Kuwa

fitaccen jarumin kannywood mai suna Tijjani asasee ya wallafa wani bidiyo inda ya ke korafi dangane da wani mataki da hukumar tace finafinai ta kano ta fitar a kansa.

A cikin sanarwar kamar yadda ya yi ikirari ya bayya cewa hukumar ta dakatar da shi bisa wasu dalilai da ya ke ganin ba su taka kara su ka karya ba.

Jarumin ya yi ikirarin cewa an dakatar da shi ne saboda fadar gaskiya da ya ke yi wanda kuma bai saba ka’ida ba.

karin bayani zai zo muku a cikin shafin mu bangaren Kannywood

0 comments on “Jaruma momee gombe ta yi nasarar siyen sabuwar mota

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *